Wutar Lantarki Na Shirin Yin Tsada a Najeriya, Gwamnatin Tarayya Ta Ce Za Ta Janye Tallafin Wuta Sannu a Hankali
Gwamnatin Tarayya ta tabbatar da cewa tana shirin janye tallafin wutar lantarki a hankali tare da aiwatar da farashin da zai dace da ainihin kuÉ—in samar da wuta a faÉ—in Najeriya.
Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara Kan Ababen More Rayuwa na Wutar Lantarki, Sadiq Wanka, ne ya bayyana hakan a wani taro da Sahara Group ta shirya a Legas.
Sadiq Wanka ya ce gwamnati za ta kare gidajen marasa ƙarfi da masu ƙaramin ƙarfi ta hanyar samar da tallafi na musamman domin rage musu tasirin karin kuɗin wutar. Ya ƙara da cewa an fara wannan sauyi ne da masu amfani da Band A, kuma ana sa ran za a faɗaɗa shi zuwa sauran rukunan masu amfani cikin kusan shekara guda.
Ya bayyana cewa Najeriya na buƙatar tsakanin dala biliyan 9 zuwa 12 a duk shekara har zuwa shekarar 2045 domin inganta bangaren wutar lantarki, yayin da ƙasar ke samun kusan dala biliyan 1 kacal a duk shekara a halin yanzu.
A cewarsa, ana hasashen bangaren wutar lantarki zai buÆ™aci jimillar jarin kusan dala biliyan 121 cikin shekaru 20 masu zuwa domin samar da isasshiyar wuta ga ‘yan Najeriya da kuma tallafa wa ci gaban tattalin arziki.





