TSOKACI: Buhari ya yi ƙoƙarin kare El-Rufai, amma El-Rufai bai fahimci manufar jagoran nasa ba
Lokacin da Muhammadu Buhari da Godwin Emefiele suka ƙaddamar da sauya fasalin takardun kuɗin Naira, wasu na ganin an yi hakan ne da tunanin cewa Bola Ahmed Tinubu ya riga ya tara tsoffin kuɗaɗe da za su ba shi damar gudanar da yaƙin neman zaɓensa.
Sai dai wanda ya jagoranci gwamnoni wajen ƙalubalantar wannan mataki a kotu shi ne tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai. Hakan ya kai ga shari’ar Attorney General of Kaduna State & 15 Others v. Attorney General of the Federation (2023).
Haka kuma, lokacin da tsohon shugaban APC na ƙasa, Abdullahi Adamu, tare da Buhari suka yi yunƙurin gabatar da Ahmed Lawan a matsayin ɗan takarar bai ɗaya na jam’iyyar APC, El-Rufai ne ya haɗa kan gwamnonin Arewa suka hana hakan.
A lokacin jawabin Bola Tinubu a Chatham House ma, lokacin da aka yi masa tambayoyi masu wahala, El-Rufai ya taka rawa wajen kare shi.
Idan aka waiwayi waɗannan abubuwa a yau, akwai abin tunani.
Yanzu Buhari ba ya raye, kuma El-Rufai na fuskantar yanayin siyasar da wasu ke ganin shi kansa ya taimaka wajen gina ta.
Wasu na ganin da Buhari yana raye, watakila da ya shiga tsakani. Amma yanzu al’amura sun sauya, kuma El-Rufai na ci gaba da fuskantar sakamakon wasu daga cikin matakan siyasar da ya taka rawa a cikinsu.
Fassarar Tsokacin Ekene Aninze, Esq.





