APC Za Ta Yi Amfani da Cikakken Ƙarfinta Domin Lashe Zaɓen 2027 – Nentawe Yilwatda

APC Za Ta Yi Amfani da Cikakken Ƙarfinta Domin Lashe Zaɓen 2027 Daga Kan Shugaban Kasa Har Kansila – Nentawe Yilwatda

Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa, Nentawe Yilwatda, ya bayyana cewa jam’iyyar za ta yi amfani da dukkan ƙarfinta na siyasa domin tabbatar da nasara a zaɓukan shekarar 2027 daga matakin kansila har zuwa kujerar shugaban ƙasa.

Yilwatda ya ce zaɓen gwamnan jihar Osun da za a gudanar a ranar 15 ga Agusta, 2026, zai zama gwajin ƙarfin jam’iyyar da kuma shirin tunkarar babban zaɓen 2027. Ya jaddada cewa lashe zaɓen Osun wajibi ne ga APC.

A cewarsa, APC tana da ƙarfin shugabanci, tsari da kuma damar lashe zaɓe a dukkan matakai, tare da bayyana cewa za a tattara gwamnoni, ‘yan majalisu da sauran shugabannin jam’iyyar domin gudanar da kamfen daga gida zuwa gida a faɗin jihar Osun.

Ya kuma yi kira ga kwamitin yaƙin neman zaɓen jam’iyyar da ya haɗa kai wajen tara albarkatu, wayar da kan masu kaɗa ƙuri’a da kuma tabbatar da nasarar ɗan takarar APC a jihar.

A nasa jawabin, shugaban kwamitin yaƙin neman zaɓen APC kuma gwamnan jihar Imo, Hope Uzodimma, ya ce jam’iyyar za ta gudanar da kamfen cikin lumana ba tare da tashin hankali ba, tare da tabbatar da cewa za ta dawo da jihar Osun ƙarƙashin ikon APC.

Uzodimma ya ce APC za ta mayar da hankali wajen tattaunawa da al’umma, ma’aikata, manoma, ‘yan kasuwa, matasa, sarakuna da shugabannin addini, yana mai cewa jam’iyyar ba za ta bari zarge-zarge ko yaɗa bayanan ƙarya daga adawa su karkatar da hankalinta ba.

Taron ƙaddamar da kwamitin ya samu halartar gwamnonin jihohin Ekiti, Yobe, Jigawa da Kano, tare da sauran manyan jiga-jigan jam’iyyar APC.

DA DUMI-DUMI

Tsoron Talauci Na Jefa Mutane Da Dama Cikin Matsananciyar Damuwa – Masana

Tsoron Talauci Na Jefa Mutane Da Dama Cikin Matsananciyar Damuwa – Masana

Aliko Dangote Ya Yi Wasiyyar A Ware Kashi Ɗaya Bisa Uku Na Dukiyarsa, Kimanin Naira Tiriliyan 16, Domin Ayyukan Jin Ƙai — Halima Dangote

Aliko Dangote Ya Yi Wasiyyar A Ware Kashi Ɗaya Bisa Uku Na Dukiyarsa Domin Ayyukan Jin Ƙai — Halima Dangote

Kyaftin ɗin Super Falcons, Rashidat Ajibade, sanye da dankwali da aka rubuta “JESUS”

Kyaftin ɗin Super Falcons, Rashidat Ajibade, na bayyana bangaskiyarta ga Yesu a duk inda ta je.

Har Tsawon Wane Lokaci Za a Iya Ajiye Kifi a Firiza Kafin Ya Lalace?

Yawan Lokacin da Kifi Zai Iya Ɗauka a Firiza Kafin Ya Lalace

Wani Magidanci a Kano Ya Kashe Wani Mutum Saboda Ya Yi Zargin Yana Neman Matarsa – Kiyawa

Wani Magidanci a Kano Ya Kashe Wani Mutum Saboda Ya Yi Zargin Yana Neman Matarsa – Kiyawa

Kanun Labarai

Budurwa Ta Yanke Gaban Saurayinta a Kano Bayan Ya Shaida Mata Zai Auri Wata – Rundunar Yan Sanda

Budurwa Ta Yanke Gaban Saurayinta a Kano Bayan Ya Sanar da Ita Cewa Zai Auri Wata — Rundunar 'Yan Sanda

Mata Sun Fi Maza Cika Alƙawarin Biyan Bashi – Inji Rahoton Moniepoint

Moniepoint ta ce alkaluman sun nuna cewa, duk da matsalolin da mata ke fuskanta wajen samun rance saboda buƙatar jingina ko rashin tarihin bashi, suna daga cikin rukunin masu kasuwanci da suka fi nuna amana wajen biyan bashin da suka karɓa.
spot_img

Labarai masu alaka

Sauran bangarori

spot_imgspot_img