A Daina Kashe Kuɗi Kan Biskit, A Riƙa Saya Wa Yara Ƙwai Ya Fi Amfani -Masana Sun Shawarci Iyaye
Daga Wakiliya
Masana harkar abinci mai gina jiki sun buƙaci iyaye su rage kashe kuɗi wajen sayen biskit, alewa da abubuwan sha masu yawan sukari, maimakon haka su riƙa sayen ƙwai domin ciyar da yara ‘yan ƙasa da shekara biyar.
A cewar masana, ba wa yaro ƙwai guda a kowace rana na taimakawa wajen rage matsalar ƙarancin abinci mai gina jiki (malnutrition), tare da inganta girma da bunƙasar kwakwalwa.
Sun ce duk da hauhawar farashin kayan abinci, bai kamata iyaye su hana ‘ya’yansu abinci mai muhimmanci kamar ƙwai ba, saboda yana ɗauke da sinadarai masu matuƙar amfani ga lafiyar yara.
Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta bayyana cewa ƙarancin abinci mai gina jiki na haifar da matsaloli kamar rashin girma yadda ya kamata, ƙarancin nauyi da rashin isassun bitamin da ma’adanai. Haka kuma, yawan cin abinci mara kyau na iya haddasa kiba da cututtuka kamar ciwon sukari, bugun jini da cututtukan zuciya.
WHO ta kuma ce kusan yara miliyan 150 masu shekaru ƙasa da biyar a duniya na fama da rashin girma, yayin da Najeriya ke cikin ƙasashen da ke da mafi yawan yaran da ke fuskantar wannan matsala.
A nata ɓangaren, Asusun Kula da Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya (UNICEF) ya ce rashin abinci mai gina jiki na tauye haƙƙin yara, domin ingantaccen abinci ne ke ba su damar girma, koyo da kuma cimma burinsu.
Ƙungiyar Likitocin Yara ta Najeriya (Paediatric Association of Nigeria) ta bayyana cewa sama da yara miliyan 12.3 a Najeriya na fama da matsananciyar ƙarancin abinci mai gina jiki, yayin da kusan yara 300,000 ke cikin haɗarin rasa rayukansu sakamakon matsalar.





