Mahaifiyata ta yi sana’ar sayar da Koko da kosai, kuma da shi ta raine ni gashi yau har na zama Ministan Tsaro – Christopher Musa
Ministan Tsaron Najeriya, Christopher Musa, ya bayyana cewa mahaifiyarsa ta kasance tana sayar da koko da kosai domin rainon su, yana mai cewa yana alfahari da irin wannan aiki na gaskiya da ya taimaka wajen kai shi matsayin da yake a yau.
Christopher Musa ya bayyana hakan ne yayin wani taron horaswa da tallafa wa zawarawa da matan jami’an tsaro a Barikin Lungi da ke Abuja, wanda Ma’aikatar Tsaro ta shirya tare da haɗin gwiwar Hukumar Bunƙasa Kananan da Matsakaitan Masana’antu (SMEDAN).
A cewarsa, bai kamata a raina masu sana’ar sayar da akara, akamu ko sauran ƙananan sana’o’i ba, domin su ma sana’o’i ne na halal da ke ciyar da iyalai.
“Bayan Uwargidan Shugaban Ƙasa ta ba masu sayar da kosai da sauran ‘yan kasuwa tallafi, na ji wasu suna sukar matakin. Amma ni ina alfahari da cewa mahaifiyata ta sayar da kunu, koko da kosai. Da kuɗin wannan sana’a ne ta tallafa wa mahaifina kuma ta taimaka mana har na kai matsayin Ministan Tsaro. Kada ku bari wani ya sa ku ji kunya saboda kuna sayar da akara ko akamu,” in ji Christopher Musa.
Ya ce jajircewar mahaifiyarsa da kuma ƙoƙarinta na taimaka wa iyali ta hanyar ƙaramar sana’a na daga cikin abubuwan da suka ba shi damar kai matsayin da yake a yau.
Shirin tallafa wa matan jami’an tsaron na da nufin ba su horo kan harkokin kasuwanci tare da ba su tallafin kuɗi, a wani ɓangare na ƙoƙarin Gwamnatin Tarayya na inganta rayuwar iyalan jami’an tsaro ta hanyar bunƙasa sana’o’i.





