Za mu mayar da matasa su koma noma idan na zama shugaban ƙasa -inji Obi/Kwankwaso 

DA DUMI-DUMI

Zan mayar da matasa su koma noma idan na zama shugaban ƙasa -inji Obi/Kwankwaso

Daga Wakiliya

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC), Peter Obi, ya ce idan aka zaɓe shi shugaban ƙasa a 2027, gwamnatinsa za ta mayar da hankali wajen samar wa matasa ayyukan yi ta hanyar noma da ƙananan sana’o’i.

Peter Obi ya bayyana haka ne ranar Asabar a Kaduna, yayin wani taron siyasa da NDC ta shirya, inda shi da abokin takararsa, Rabiu Kwankwaso, suka yi wa magoya bayansu bayani kan shirinsu ga Najeriya.

Ya ce gwamnatinsa za ta mayar da Najeriya daga ƙasar da ke dogaro da amfani da kaya zuwa ƙasar da ke samar da su, tare da amfani da rancen kuɗi ne kawai wajen saka hannun jari.

“Ba za mu ƙara karɓar bashi domin amfani da shi wajen kashe-kashe ba. Za mu karɓi bashi ne domin saka hannun jari da samar da ayyukan yi,” in ji shi.

Peter Obi ya ce yawan matasan Najeriya na daga cikin manyan kadarorin ƙasar, amma rashin ayyukan yi na haifar da matsaloli da dama.

Ya kwatanta Najeriya da Indonesia, inda ya ce duk da cewa Najeriya na da kimanin mutum miliyan 230, yayin da Indonesia ke da kusan miliyan 280, matasan Indonesia sun fi samun damar aiki.

“Za mu taimaka wa matasa su samu abin yi. Za mu tabbatar sun koma noma, sannan su koma ƙananan sana’o’i. Za mu tallafa musu,” in ji Peter Obi.

Ya kuma yi magana kan matsalar shaye-shayen miyagun ƙwayoyi, inda ya ce ya kamata a tsaurara hukunci kan masu safarar ƙwayoyi.

Peter Obi ya ce idan aka zaɓe shi, gwamnatinsa za ta tanadi hukuncin ɗaurin rai da rai ga masu safarar miyagun ƙwayoyi da ke barazana ga rayuwar matasa.

Ya kuma ce yawan amfani da miyagun ƙwayoyi a Najeriya ya fi matsakaicin abin da ake samu a duniya, yana mai danganta hakan da matsalar rashin aikin yi da ke addabar matasa.

Peter Obi da Rabiu Kwankwaso na daga cikin ‘yan siyasar da suka bayyana aniyarsu ta neman shugabancin Najeriya a zaɓen 2027.

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

BRAZIL: Mutumin da matarsa ta yanke wa azzakari zai sake aurenta

Yanzu haka, Gilberto na shirin sake aurenta, inda zai yi amfani da kuɗin diyya da ya samu bayan an yaɗa hotunan raunukan da ya samu a intanet ba tare da izininsa na yaɗawa ba.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img