Shugaba Bola Ahmed Tinubu na cewa tattalin arzikin Najeriya ya farfaɗo, ƙasar ta tsira daga barazanar durƙushewa, kuma rayuwar jama’a na ci gaba da inganta. Amma idan aka dubi halin da talakawa ke ciki, da wuya a ga hujjar da ke tabbatar da wannan ikirari.
Talakawa ba sa auna ingancin tattalin arziki da alkaluman gwamnati. Abin da suke kalla shi ne farashin abinci, man fetur da sauran muhimman kayan masarufi. A yau kuwa, kusan komai ya yi tsada, kuma rayuwa ta ƙara tsananta ga mafi yawan ‘yan Najeriya.
Tun bayan cire tallafin man fetur a shekarar 2023, farashin fetur ya ci gaba da ƙaruwa, abin da ya jawo hauhawar farashin kusan dukkan kayayyaki da hidimomi. Haka kuma, farashin abinci da na gas ɗin girki sun kai matakin da ya sa iyalai da dama ke fama da wahalar ciyar da kansu.
A irin wannan yanayi, yana da wuya a ce rayuwa na inganta ko kuma wadata na tafe, domin mafi yawan abin da mutane ke samu yana ƙarewa ne wajen biyan buƙatun yau da kullum, ba tare da damar yin tanadi ba.
Har ila yau, akwai tambayoyi kan yadda ake aiwatar da kasafin kuɗin gwamnati. Duk da rahotannin cewa kuɗaɗen shiga sun zarce yadda aka tsara, har yanzu ana samun jinkiri wajen aiwatar da kasafin kuɗi da ayyukan raya ƙasa.
Sanata Tahir Monguno na jam’iyyar APC ma ya yi tambayar inda kuɗaɗen shiga suke tafiya idan har gwamnati na samun kuɗi fiye da yadda aka yi hasashe, amma aiwatar da kasafin kuɗi na tafiya a hankali. A cewarsa, idan ba a aiwatar da kasafin kuɗi yadda ya kamata ba, to jama’a ba za su ga amfanin dimokuraɗiyya ba.
A taƙaice, yayin da gwamnati ke ganin tattalin arzikin ƙasa na kan hanya mai kyau, abin da talakawan Najeriya ke fuskanta a rayuwarsu ta yau da kullum ya nuna cewa har yanzu wahala ce ta fi bayyana fiye da sauƙin rayuwa.
Fassarar Sharhin Marubuci, Adekunle Adekoya




