“Me Ya Hana Ki Ba Sani Danja Dama Ta Biyu?” – Jama’a Sun Yi Wa Mansura Isah Zafafan Martani Bayan Ta Nemi A Sake Ba Tinubu Dama
Daga Wakiliya
Fitacciyar jarumar Kannywood, Mansura Isah, ta janyo ce-ce-ku-ce bayan ta bayyana dalilan da suka sa take ganin ya kamata a sake bai wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Mataimakinsa Kashim Shettima dama a 2027.
Mansura ta wallafa hotonta tare da Shettima, inda ta rubuta: “Why we should give them a second chance.”
Ta jero NELFUND, gyaran hanyoyi, tallafa wa manoma, dialysis, yaki da Boko Haram, tallafin masu rauni, daidaiton tattalin arziki da darajar Dala cikin abubuwan da ta bayyana a matsayin nasarorin gwamnati.
Sai dai sakon ya janyo zafafan martani, inda wasu suka kalubalanci ikirarin, wasu kuma suka mayar da magana kan tsohon mijinta, Sani Danja.
Daya daga cikin tambayoyin da suka fi daukar hankali shi ne:
“Me ya hana ki ba Sani Danja dama ta biyu?”
Wasu kuma sun kalubalanci Mansura ta yi tafiya zuwa wasu sassan Najeriya a mota tunda ta ce an samu sauyi a batun tsaro, muna so Mansura ta yi tafiya zuwa wasu sassan Borno, Zamfara, Niger, Katsina da Kudancin Kaduna.
Sakon Mansura ya koma batun muhawara kan ayyukan gwamnatin Tinubu da kuma yiwuwar sake zaben Tinubu da Shettima a 2027.




