Mailantarki ya ayyana kansa a matsayin wanda ya yi nasara a zaben fidda Gwani – ya sha alwashin shigar da sabuwar kara

DA DUMI-DUMI

GOMBE PDP: Mailantarki ya bayyana kansa a matsayin wanda ya yi nasara a zaben fidda Gwani – ya sha alwashin shigar da sabuwar kara kan Pantami

Daga Wakiliya

Khamisu Ahmed Mailantarki ya bayyana kansa a matsayin wanda ya yi nasara a zaɓen fidda gwani na PDP da aka gudanar a Gombe, duk da cewa kwamitin zaɓen jam’iyyar ya sanar da Farfesa Isa Ali Pantami a matsayin wanda ya lashe zaɓen.

Mailantarki ya ce zai sake komawa kotu domin ƙalubalantar sakamakon da kuma halaccin shigar Pantami cikin takarar, inda ya sha alwashin ci gaba da fafutukar neman haƙƙinsa ta hanyar doka.

Pantami ya samu rinjaye a sakamakon da kwamitin jam’iyyar ya sanar, inda ya samu kuri’u 2,024, Mailantarki kuma ya samu 389, yayin da Usman Aliyu Garry ya samu 112.

Me zaku ce akai ? ~ Wakiliya

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

BRAZIL: Mutumin da matarsa ta yanke wa azzakari zai sake aurenta

Yanzu haka, Gilberto na shirin sake aurenta, inda zai yi amfani da kuɗin diyya da ya samu bayan an yaɗa hotunan raunukan da ya samu a intanet ba tare da izininsa na yaɗawa ba.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img