“Ko dai Lagos yake nufi, ya yi ɗimuwa ya ce Arewa?” — ACF ta soki Tinubu kan ikirarin cewa Arewa ce ta fi cin gajiyar gwamnatinsa

DA DUMI-DUMI

“Ko dai Lagos yake nufi, ya yi ɗimuwa ya ce Arewa?” — ACF ta soki Tinubu kan ikirarin cewa Arewa ce ta fi cin gajiyar gwamnatinsa

Daga Wakiliya

Ƙungiyar Arewa Consultative Forum (ACF) ta soki ikirarin Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu cewa Arewa ce ta fi kowace shiyya cin gajiyar sauye-sauyen tattalin arzikinsa.

Ƙungiyar ta ce kalaman shugaban ba su yi daidai da halin da miliyoyin al’ummar Arewa ke ciki ba, musamman wajen talauci, rashin tsaro, noma da kuma abubuwan more rayuwa.

Mai magana da yawun ACF, Farfesa Tukur Muhammad Baba, ya ce ikirarin shugaban bai zo da cikakkun bayanai da za a iya tantancewa ba.

Ya ce: “Ko dai Lagos yake nufi ne ya yi ɗimuwa da Arewa?” yana mai cewa matsalolin talauci, rashin tsaro, koma bayan noma da kuma rashin ingantattun ababen more rayuwa na ci gaba da addabar yankin.

Farfesa Baba ya ce noma a Arewa ya shiga cikin mawuyacin hali sakamakon matsalolin tsaro da kuma shigo da kayan abinci daga ƙasashen waje.

Ya kuma yi zargin cewa rabon muƙaman gwamnatin tarayya da kuma ayyukan raya ƙasa ba su nuna cewa Arewa ce ta fi cin gajiyar gwamnatin ba.

Ya ce akwai matsalolin tituna, yawan yaran da ba sa zuwa makaranta da kuma ƙaruwar talauci a yankin.

Farfesa Baba ya shawarci Shugaba Tinubu da ya nemi bayanai daga wasu hanyoyi idan ikirarinsa ya samo asali ne daga bayanan da jami’an gwamnatinsa suka gabatar masa.

Ya ce watakila jami’an na ɓoye masa gaskiyar halin da ake ciki ko kuma suna ba shi bayanan da ka iya jefa gwamnatinsa cikin abin kunya.

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

Gwamnatin Najeriya za ta fara biyan tsoffin ma’aikatan Nigeria Airways Naira biliyan 18

Sai dai ya bayyana cewa gwamnati za ta biya kuɗin da aka tantance kuma aka tabbatar da shi, ba tare da ƙarin kuɗin da ya dace da hauhawar farashi na tsawon shekaru 20 ba.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img