Ƙasar Guinea ta sanar da cewa ba za ta shiga tsarin amfani da sabuwar kuɗin bai ɗaya ta ƙungiyar ECOWAS mai suna Eco ba.
ECOWAS na shirin ƙaddamar da kuɗin Eco a watan Yulin shekarar 2027, amma ƙasashen da suka cika wasu sharuɗɗa ne kawai za su fara amfani da ita. Sharuɗɗan sun haɗa da daidaiton hauhawar farashi, bashi da kuma tsarin kuɗi.
Guinea ita ce ƙasa ta farko a cikin mambobin ECOWAS da ta fito fili ta ce za ta ci gaba da amfani da kuɗinta na ƙasa, wato Guinean Franc.
Masana tattalin arziƙi sun bayyana cewa gwamnatin Guinea na ganin shiga tsarin bai ɗaya tun yanzu na iya kawo cikas ga tattalin arziƙinta, saboda har yanzu ƙasar ba ta kai matakin samar da kayayyaki da zai ba ta damar cin gajiyar tsarin ba.
Haka kuma, kusan kashi 80 cikin 100 na kayayyakin da Guinea ke fitarwa ana sayar da su ne zuwa ƙasashen Asiya, ba ƙasashen Yammacin Afirka ba. Saboda haka, masana na ganin ci gaba da amfani da kuɗinta zai ba ta damar ci gaba da sarrafa manufofin tattalin arziƙinta yadda take so.
Ana sa ran shugabannin ECOWAS za su sake ganawa a watan Disamba domin tattauna sauran batutuwan da suka rage kafin fara amfani da kuɗin Eco.




