Gaggawar Yaɗa Labaran da Ba a Tantance Ba Ka Iya Shafar Kasuwar Makamashi da Zuba Jari, Ya Jawo Tashin Farashi – NUPRC Ta Gargadi Kafafen Yaɗa Labarai

Daga Wakiliya

Hukumar Kula da Harkokin Fetur ta Ƙasa (NUPRC) ta gargadi kafafen yaɗa labarai da su guji wallafa rahotannin da ba a tabbatar da ingancinsu ba, tana mai cewa irin waɗannan labarai na iya shafar kasuwar makamashi, zuba jari da kuma ra’ayin jama’a kafin a tantance gaskiyar lamarin.

Babbar Jami’ar Hukumar, Engr. Oritsemeyiwa Eyesan, ta bayyana hakan ne a wani taron horaswa na Society of Petroleum Engineers (SPE) Nigeria Council da aka gudanar a Legas. Mataimakin Daraktan Kula da Filayen Mai, Amba Ndoma-Egba, ne ya wakilce ta.

Eyesan ta ce a wannan zamani, bayanan da ba a tantance ba na yaɗuwa cikin sauri fiye da yadda ake iya tabbatar da sahihancinsu, lamarin da ka iya tasiri kan kasuwannin makamashi da shawarar masu zuba jari.

Ta jaddada cewa gina ingantaccen labari game da harkokin man fetur ba aikin kafafen yaɗa labarai kaɗai ba ne, illa haɗin gwiwar masu tsara dokoki, kamfanonin mai, masu zuba jari da kuma ‘yan jarida.

Ta ƙara da cewa dokar Petroleum Industry Act (PIA) ta 2021 ta ɗora wa NUPRC alhakin gudanar da harkokin mai cikin gaskiya, bayyananniyar hanya da kuma bisa ƙa’idojin duniya domin ƙarfafa amincewar masu zuba jari.

Dangane da zagayen bayar da lasisin haƙar mai na shekarar 2025, Eyesan ta bayyana cewa an bayar da filayen mai guda 50, yayin da kamfanoni 196 suka tsallake matakin tantancewa, sannan kamfanoni 143 suka gabatar da tayi guda 200 kan kadarori 37.

Sai dai ta nuna damuwa cewa wasu rahotanni da aka wallafa kan wannan shiri sun dogara ne da hasashe da bayanan da ba a tabbatar da su ba, abin da ya haifar da rashin fahimta a tsakanin jama’a.

A ƙarshe, ta buƙaci ‘yan jaridar da ke ba da rahotannin makamashi su mayar da hankali kan tantance bayanai, fahimtar alkaluma da kuma bayar da cikakken mahallin labari domin tabbatar da sahihanci da ƙarfafa amincewar jama’a.

DA DUMI-DUMI

Kasar Guinea Ta Fice Daga Shirin Samar da Kuɗin Bai Ɗaya na ECOWAS -Ta Zabi Riƙe Kuɗinta

Ana sa ran shugabannin ECOWAS za su sake ganawa a watan Disamba domin tattauna sauran batutuwan da suka rage kafin fara amfani da kuɗin Eco.

Najeriya Ba Ta da Tattalin Kula da Abubuwan Da Aka Gina, Shi Yasa Kasar Ta Kasa Ci Gaba – Okonjo-Iweala

Mu a Najeriya ba mu da kyakkyawar al'adar kula da abubuwan da muka gina. Ni ma 'yar Najeriya ce, amma dole ne mu faɗi gaskiya," in ji ta.

Wani Mutum da ‘Yan Sanda Suka Baza Hotonsa Suna Nemansa Ruwa a Jallo Ya Sake Aika Musu Sabon Hoto, Ya Ce Wanda Suka Saka...

"Ga hoto na mai kyau ku canza. Wanda kuka saka ba ya min kyau kwata-kwata."

Malamin da ya shiga siyasa, aka yi ƙwaramniyar siyasa da shi, ya fi malamin da ya zauna kan buzun yana yi wa ‘yan siyasa...

Malamin da ya shiga siyasa, aka yi ƙwaramniyar siyasa da shi, ya fi malamin da ya zauna kan buzun yana yi wa 'yan siyasa addu'a -Dr. Ahmed Gumi

An Kashe Biliyoyin Naira Amma Duk da Haka Cibiyoyin Lafiya 6,516 Sun Gagara Aiki a Najeriya; Arewa Ce Kan Gaba

Jihar Katsina ce ke da mafi yawan cibiyoyin da ba sa aiki da guda 442, sai Osun da 406, yayin da Benue ke da 343, Enugu 335, Adamawa 286, sannan Borno na cikin jerin jihohin da ke fuskantar matsala.

Kanun Labarai

Kasar Guinea Ta Fice Daga Shirin Samar da Kuɗin Bai Ɗaya na ECOWAS -Ta Zabi Riƙe Kuɗinta

Ana sa ran shugabannin ECOWAS za su sake ganawa a watan Disamba domin tattauna sauran batutuwan da suka rage kafin fara amfani da kuɗin Eco.

Najeriya Ba Ta da Tattalin Kula da Abubuwan Da Aka Gina, Shi Yasa Kasar Ta Kasa Ci Gaba – Okonjo-Iweala

Mu a Najeriya ba mu da kyakkyawar al'adar kula da abubuwan da muka gina. Ni ma 'yar Najeriya ce, amma dole ne mu faɗi gaskiya," in ji ta.

Malamin da ya shiga siyasa, aka yi ƙwaramniyar siyasa da shi, ya fi malamin da ya zauna kan buzun yana yi wa ‘yan siyasa...

Malamin da ya shiga siyasa, aka yi ƙwaramniyar siyasa da shi, ya fi malamin da ya zauna kan buzun yana yi wa 'yan siyasa addu'a -Dr. Ahmed Gumi

An Kashe Biliyoyin Naira Amma Duk da Haka Cibiyoyin Lafiya 6,516 Sun Gagara Aiki a Najeriya; Arewa Ce Kan Gaba

Jihar Katsina ce ke da mafi yawan cibiyoyin da ba sa aiki da guda 442, sai Osun da 406, yayin da Benue ke da 343, Enugu 335, Adamawa 286, sannan Borno na cikin jerin jihohin da ke fuskantar matsala.

Tsadar Sadaki Na Sa Matasa Da Dama Gujewa Yin Aure – Shugaban Uganda Ya Gargadi Iyaye Su Rage Sadakin ‘Ya’yansu

Ku mutanen Banyankole kuna lalata ci gaban yawan jama'a. Iyaye, me ya sa kuke sayar da 'ya'yanku? Shanu 16, ban ma san adadin sauran ba. Me ya sa dole ne ku tara dukiya ta hanyar 'ya'yanku? Me ya sa ba za ku yi aiki ku sami abin ku da kanku ba?" in ji Museveni.

Kada A Rika Ba Jarirai Yan Ƙasa da Wata Shida Abinci Mai Tauri Kamar Tuwo, Koko, Kunu ko Fura – Likitocin Yara Sun Gargadi...

hakan na iya jefa su cikin haɗarin ƙarancin jini (anaemia), kamuwa da cututtuka da kuma shaƙewa.

NACCIMA Ta Buɗe Shirin Bayar da Rancen Dala Miliyan 150 Ga Kamfanonin Najeriya

NACCIMA ta ce shirin na da nufin sauƙaƙa wa kamfanonin Najeriya samun jari na dogon lokaci daga ƙasashen waje domin bunƙasa masana'antu da ƙarfafa tattalin arzikin ƙasa.
spot_img

Labarai masu alaka

Sauran bangarori

spot_imgspot_img