Kada A Rika Ba Jarirai Yan Ƙasa da Wata Shida Abinci Mai Tauri Kamar Tuwo, Koko, Kunu ko Fura – Likitocin Yara Sun Gargadi Iyaye
Daga Wakiliya
Likitocin kula da lafiyar yara sun gargadi iyaye da masu renon yara da su guji bai wa jarirai yan ƙasa da watanni shida abinci mai tauri ko na ƙari, suna cewa hakan na iya jefa su cikin haɗarin ƙarancin jini (anaemia), kamuwa da cututtuka da kuma shaƙewa.
Masanan sun bayyana cewa bai wa jarirai abinci irin su tuwo, fura, koko, eba ko sauran nau’ikan abinci kafin su kai wata shida na rage yawan nonon uwa da suke sha, alhali nonon uwa ne ke ɗauke da muhimman sinadarai da garkuwar jiki da jariri ke buƙata a wannan mataki.
Shugaban Sashen Kula da Lafiyar Yara na Asibitin Koyarwa na Tarayya da ke Katsina, Dr. Abdurrazzaq Alege, ya ce jarirai kafin wata shida ba su kware wajen haɗiye abinci ba, don haka ba su abinci mai tauri na iya sa su shaƙe.
Ya ƙara da cewa maye gurbin nonon uwa da abinci mai yawan carbohydrates kawai na iya haifar da ƙarancin sinadarin iron da sauran muhimman abubuwan gina jiki, lamarin da kan janyo rashin girma yadda ya kamata da ƙarancin jini.
Shi ma ƙwararren likitan yara, Dr. Ayodele Renner, ya ce babu wani amfani na musamman da abinci irin su eba ko makamantansu ke da shi ga jarirai yan ƙasa da watanni shida, domin ba sa samar musu da sinadaran iron, zinc da bitamin da suke buƙata.
Ya shawarci iyaye su ci gaba da ba jarirai nonon uwa kaɗai har sai sun kai wata shida. Idan kuma nonon uwa bai wadatar ba, ya ce a nemi shawarar likita domin amfani da madarar jarirai (infant formula), maimakon fara ba su abinci tun da wuri.
Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ba da shawarar cewa jarirai su riƙa shan nonon uwa kaɗai na tsawon watanni shida na farko, ba tare da ba su ruwa ko wani nau’in abinci ba, sai dai idan likita ya ba da umarni.





