Gilashi ya fashe: Jirgin da aka tura kwaso ‘yan Najeriya daga Afirka ta Kudu ya kasa tashi bayan saukarsa acen

DA DUMI-DUMI

Daga Wakiliya


An samu tsaiko a aikin kwaso wasu ‘yan Najeriya 271 daga Afirka ta Kudu bayan an gano tsagewa a gilashin gaban ɗakin matuƙan jirgin (cockpit), lamarin da ya hana jirgin tashi daga birnin Johannesburg.

Mai magana da yawun Ma’aikatar Harkokin Wajen Najeriya, Kimiebi Imomotimi Ebienfa, ya ce an dakatar da tashin jirgin ne domin tabbatar da tsaron fasinjoji, yana mai cewa kamfanin Air Peace ya shirya tura wani jirgi domin ci gaba da aikin kwaso mutanen.

Ebienfa ya bayyana cewa an shirya jirgin ne domin dawo da ‘yan Najeriya 271, amma aka gano matsalar ne kafin tashinsa.

Ya kuma nemi afuwar waɗanda abin ya shafa, yana mai tabbatar da cewa za a tura wani jirgi cikin gaggawa domin kammala aikin.

Tun bayan sabbin hare-haren da ake kai wa baƙin haure a Afirka ta Kudu, gwamnatin tarayya ta ce ta riga ta kwaso ‘yan Najeriya 859 zuwa gida lafiya.

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

Gwamnatin Najeriya za ta fara biyan tsoffin ma’aikatan Nigeria Airways Naira biliyan 18

Sai dai ya bayyana cewa gwamnati za ta biya kuɗin da aka tantance kuma aka tabbatar da shi, ba tare da ƙarin kuɗin da ya dace da hauhawar farashi na tsawon shekaru 20 ba.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img