Babu inda Kotu ta hana ni ganin mutane a asibiti, El-Rufai ya nemi ICPC ta janye zargin da ta yi akansa na karya umarnin Kotu

Daga Wakiliya

Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya musanta zargin da Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (ICPC) ta yi masa na cewa ya karya umarnin kotu tare da amfani da damar zuwa jinya ba bisa ƙa’ida ba.

A wata sanarwa da mai ba shi shawara kan yaɗa labarai, Muyiwa Adekeye, ya fitar a ranar Laraba, El-Rufai ya ce sanarwar da ICPC ta fitar ranar 7 ga Yuli ta ƙunshi bayanan da ba su dace da gaskiya ko doka ba.

Sanarwar ta ce rashin halartar El-Rufai zaman kotu ya samo asali ne daga matsalar rashin lafiya da aka sanar da ICPC tun kafin zaman kotun, tare da zargin cewa an hana likitansa na kashin kansa, Farfesa Bello Abubakar, damar duba lafiyarsa.

El-Rufai ya ce buƙatar kai shi Asibitin Ƙasa da ke Abuja domin duba lafiyarsa ta riga ta kasance kafin sanar da shi ranar zaman kotu, kuma hakan ya yi daidai da umarnin kotu da ya ba shi damar samun kulawar lafiya.

Ya kuma musanta cewa ya karya wani umarnin kotu yayin da yake asibiti, yana mai cewa babu wani umarni da ya hana mutane ziyartar sa yayin jinya.

Haka kuma, ya nemi ICPC ta bayyana dalilin kama Farfesa Bello Abubakar tare da sakin sa ba tare da wani sharaɗi ba idan ba ta da hujjojin zargin da take masa.

A ƙarshe, El-Rufai ya buƙaci ICPC ta janye sanarwar da ta fitar tana zarginsa da karya umarnin kotu, yana mai jaddada cewa zai ci gaba da kare haƙƙinsa na samun shari’a ta adalci da kuma kulawar lafiya bisa tanadin doka.

DA DUMI-DUMI

APC Za Ta Yi Amfani da Cikakken Ƙarfinta Domin Lashe Zaɓen 2027 – Nentawe Yilwatda

APC Za Ta Yi Amfani da Cikakken Ƙarfinta Domin Lashe Zaɓen 2027 Daga Kan Shugaban Kasa Har Kansila - Nentawe Yilwatda

Tsoron Talauci Na Jefa Mutane Da Dama Cikin Matsananciyar Damuwa – Masana

Tsoron Talauci Na Jefa Mutane Da Dama Cikin Matsananciyar Damuwa – Masana

Aliko Dangote Ya Yi Wasiyyar A Ware Kashi Ɗaya Bisa Uku Na Dukiyarsa, Kimanin Naira Tiriliyan 16, Domin Ayyukan Jin Ƙai — Halima Dangote

Aliko Dangote Ya Yi Wasiyyar A Ware Kashi Ɗaya Bisa Uku Na Dukiyarsa Domin Ayyukan Jin Ƙai — Halima Dangote

Kyaftin ɗin Super Falcons, Rashidat Ajibade, sanye da dankwali da aka rubuta “JESUS”

Kyaftin ɗin Super Falcons, Rashidat Ajibade, na bayyana bangaskiyarta ga Yesu a duk inda ta je.

Har Tsawon Wane Lokaci Za a Iya Ajiye Kifi a Firiza Kafin Ya Lalace?

Yawan Lokacin da Kifi Zai Iya Ɗauka a Firiza Kafin Ya Lalace

Kanun Labarai

Wani Magidanci a Kano Ya Kashe Wani Mutum Saboda Ya Yi Zargin Yana Neman Matarsa – Kiyawa

Wani Magidanci a Kano Ya Kashe Wani Mutum Saboda Ya Yi Zargin Yana Neman Matarsa – Kiyawa

Budurwa Ta Yanke Gaban Saurayinta a Kano Bayan Ya Shaida Mata Zai Auri Wata – Rundunar Yan Sanda

Budurwa Ta Yanke Gaban Saurayinta a Kano Bayan Ya Sanar da Ita Cewa Zai Auri Wata — Rundunar 'Yan Sanda

Mata Sun Fi Maza Cika Alƙawarin Biyan Bashi – Inji Rahoton Moniepoint

Moniepoint ta ce alkaluman sun nuna cewa, duk da matsalolin da mata ke fuskanta wajen samun rance saboda buƙatar jingina ko rashin tarihin bashi, suna daga cikin rukunin masu kasuwanci da suka fi nuna amana wajen biyan bashin da suka karɓa.
spot_img

Labarai masu alaka

Sauran bangarori

spot_imgspot_img