Duk mijin da ya tilasta wa matarsa yin jima’i ba tare da amincewarta ba, na iya fuskantar ɗaurin rai-da-rai – Gwamnatin Lagos
Daga Wakiliya
Gwamnatin Jihar Legas ta gargadi maza da su guji tilasta wa matansu yin jima’i ba tare da yardarsu ba, tana mai cewa hakan na iya kai wa ga hukuncin daurin rai da rai a karkashin dokokin jihar.
Daraktan Masu Shigar da Kara na Jihar Legas (DPP), Dakta Babajide Martins, ne ya yi wannan gargadin yayin wani taro da aka gudanar domin fara watan wayar da kan jama’a game da rikicin cikin gida da cin zarafin mata da yara.
Da yake amsa tambaya kan ko mace mai aure za ta iya kai karar mijinta bisa zargin fyade idan ya yi lalata da ita ba tare da yardarta ba, Martins ya ce dokar Najeriya ba ta amince da laifin fyade tsakanin ma’aurata kai tsaye ba.
Sai dai ya ce Dokar Laifuka ta Jihar Legas ta tanadi wani laifi mai suna “cin zarafin jima’i ta hanyar kutsawa” (sexual assault by penetration), wanda hukuncinsa zai iya kai wa daurin rai da rai.
Ya ce hakan na nufin mijin da ya tilasta wa matarsa yin jima’i bayan ta nuna ba ta yarda ba, zai iya fuskantar tuhuma karkashin wannan tanadin doka.
“Duk mutumin da yake ganin saboda ya biya sadakin matarsa babu wanda zai iya kalubalantar sa kan cin zarafinta, ya kamata matar ta kai rahotonsa ga Hukumar Yaki da Rikicin Cikin Gida da Cin Zarafin Jima’i,” in ji shi.
Martins ya kara da cewa dokar ta bambanta tsakanin fyade da tilasta jima’i ta hanyar kutsawa idan abin ya shafi ma’aurata.
Ya ce idan ma’aurata suna tare cikin zaman lafiya, ba za a tuhumi miji da fyade ga matarsa ba, amma idan wata matsala ta taso kuma matar ta ki amincewa da yin jima’i, bai halatta mijin ya tilasta mata ba.
“Idan mijin ya tilasta mata kuma ta kai rahoto, ba za mu tuhume shi da fyade ba, sai dai da laifin cin zarafin jima’i ta hanyar kutsawa, kuma hukuncinsa na iya zama daurin rai da rai,” in ji DPP ɗin.
Ya bukaci matan da ke fuskantar kowace irin matsalar cin zarafi a cikin gida ko ta jima’i da su kai rahoto ga Hukumar Yaki da Rikicin Cikin Gida da Cin Zarafin Jima’i domin daukar matakin da ya dace.




