Binciken Wutar Mambilla: EFCC ta kafa babbar tawaga don binciken Atiku, Malami da wasu jiga-jigai
Daga Wakiliya
Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa, EFCC, ta kafa wata tawaga ta musamman domin binciken wasu jiga-jigan Najeriya da aka ambata a hukuncin kotun sasantawa ta ICC kan aikin samar da wutar lantarki na Mambilla.
Wakiliya ta ruwaito Jaridar Premium Times ta ce cikin mutanen da aka ambata akwai tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, tsohon Ministan Shari’a Abubakar Malami, tsohon Ministan Wuta Olu Agunloye da tsohon Mai bawa Shugaban Ƙasa Shawara kan Tsaro (NSA), Sambo Dasuki.
Rahoton ya ce ana zargin wasu daga cikin mutanen da alaƙa da wasu kuɗaɗe da mu’amaloli da Leno Adesanya, mai kamfanin Sunrise Power, wanda ke da alaƙa da aikin Mambilla.
Kotun sasantawar ta ICC da ke Paris ta yi watsi da da’awar Sunrise Power kan Najeriya, tare da umartar kamfanin da ya biya Najeriya dala miliyan 11.8 a matsayin kuɗin shari’a.
A game da Atiku, kotun ta yi tambayoyi kan biyan dala dubu 500,000 da Adesanya ya tura wa Jennifer Douglas, tsohuwar matar Atiku, a shekarar 2003. Kotun ta ce bayanin da Adesanya ya bayar kan dalilin biyan kuɗin bai gamsar ba kuma ya gaza gabatar da isassun takardun shaida.
Sai dai tuni Atiku ya musanta cewa kotun ta tuhume shi da aikata laifi.
A halin yanzu, majiyoyin EFCC sun ce ana iya gayyatar Atiku da wasu daga cikin mutanen domin amsa tambayoyi yayin da binciken ke gudana.
Mai magana da yawun EFCC, Dele Oyewale, ya tabbatar da rahoton kafa tawagar bincike na musamman din, amma ya ce bai samu cikakken bayani kan binciken ba.




