Binciken Aikin Wutar Mambilla: Kotun ICC ta gano yadda miliyoyin daloli da naira suka rika yawo tsakanin manyan jami’an gwamnati da iyalansu

DA DUMI-DUMI

Ga abin da ya faru kan badakalar kuɗin aikin wutar lantarki na Mambilla.

Daga Wakiliya

Wata kotun sasanci ta ƙasa da ƙasa ta ICC ta gano cewa Leno Adesanya, wanda ya kafa kamfanin Sunrise Power, ya biya ko ya tura makudan kuɗaɗe ga wasu mutane da ke da alaƙa da manyan jami’an gwamnati, yayin da yake neman mallakar aikin Mambilla.

Misali, an tura dala miliyan 1.74 ga ɗan tsohon mai ba shugaban ƙasa shawara kan tsaro, Sambo Dasuki.

An kuma tura dala 500,000 ga matar tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar, sannan aka biya tsohon ministan wutar lantarki Olu Agunloye kusan Naira miliyan 5.2.

Haka kuma, an tura Naira miliyan 10 ga Abdullahi Yola, tsohon Solicitor-General na Tarayya, da kuma sama da Naira miliyan 25 ga ɗan wata tsohuwar Sakatariyar Ma’aikatar Wutar Lantarki.

Kotun ta ce wasu daga cikin bayanan da Adesanya ya bayar kan waɗannan kuɗaɗe ba su gamsar da ita ba, kuma akwai manyan alamomin tuhuma.

Amma kotun ta jaddada cewa ba ta tabbatar da cewa duk waɗannan kuɗaɗen cin hanci ba ne.

Abin da ta tabbatar kai tsaye shi ne batun tsohon Antoni-Janar na Tarayya, Abubakar Malami.

Kotun ta ce Adesanya da Malami sun yi wata yarjejeniya ta cin hanci, inda aka yi alkawarin bai wa Malami wani kaso daga cikin dala miliyan 200 da aka shirya bai wa Sunrise.

A ƙarshe, ba a biya kuɗin ba, kuma kotun ta yi watsi da da’awar Sunrise ta dala miliyan 400, tare da umartar kamfanin da Adesanya su biya Najeriya kuɗaɗen shari’a da sasanci.

Wannan shi ne abin da rahoton kotun ya bayyana kan tafiyar kuɗin aikin Mambilla, me kuke fatan ayi?

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

Za Ka Iya Ci Gaba da Goyon Bayan Tinubu – Amma Shi Ya Damu Da Kai? Musamman Kai Dan Arewa?

Sai dai duk da waɗannan shirye-shirye, matsin tattalin arziki har yanzu yana damun miliyoyin ’yan Najeriya.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img