Mutuwar Masu Haƙar Ma’adinai: Adeyanju Ya Shiga Kwamitin Bincike, Ya Ce Zai Fallasa Duk Wani Ƙoƙarin Ɓoye Gaskiya
Daga Wakiliya
Lauyan kare haƙƙin bil’adama, Deji Adeyanju, ya amince da shiga kwamitin da gwamnatin Jihar Neja ta kafa domin binciken mutuwar wasu masu haƙar ma’adinai da ake zargin sun mutu a Minna.
Rahotanni sun ce mutane 37 da ake zargin masu haƙar zinare ba bisa ka’ida ba ne suka mutu a Minna a hannun jami’an Civil Defence, lamarin da ya jawo ce-ce-ku-ce da kira da a gudanar da cikakken bincike.
Adeyanju ya ce ya shiga kwamitin ne domin kare muradun waɗanda suka mutu da kuma tabbatar da cewa an gano ainihin abin da ya haddasa mutuwarsu.
A wata sanarwa da ya fitar, lauyan ya ce ya gode wa gwamnati bisa zaɓen da ta yi masa, amma ya jaddada cewa ba zai amince da duk wani yunƙuri na murƙushe gaskiya ko rufa-rufa ko kare waɗanda suka aikata laifi ba.
Ya kuma roƙi gwamnati da kada ta biya mambobin kwamitin wani alawus, kuɗin zama ko wata irin hidimar kuɗi, yana mai cewa aikin na ƙasa ne da ya kamata a yi shi ba tare da neman wani abin duniya ba.
Adeyanju ya ce shi da kansa zai ɗauki nauyin kuɗin otal, sufuri da sauran abubuwan da zai kashe yayin gudanar da aikin.
Ya ce idan aka yi yunƙurin kare duk wanda ke da hannu a lamarin ko ɓoye gaskiyar abin da ya faru, zai fallasa hakan.
Adeyanju ya ce waɗanda suka mutu sun cancanci a yi musu adalci, kuma bai kamata abin da ya kira “Nigerian factor” ya hana a gano gaskiyar lamarin ba.




