‘Ba ma nuna bambanci’ – inji ’Yan sandan Borno
Daga Wakiliya
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Borno ta ce ba ta goyon bayan wata jam’iyyar siyasa, tana kuma aiki ne ba tare da nuna bambanci ba.
Kakakin rundunar, ASP Nahum Kenneth Daso, ya bayyana hakan yayin wani jawabi ga manema labarai kan kama wasu mutane biyar da bisa zargin sanya rigar “Tinubu Must Go” kafin daga bisani aka ce an same su da miyagun ƙwayoyi da wasu haramtattun abubuwa.
Ya ce mutanen biyar an gurfanar da su a gaban kotu, bayan da aka kama su sanye da riguna masu ɗauke da wani rubutu “Tinubu Must Go” da ya jawo cece-kuce a tsakanin jama’a.
Daso ya ce rundunar ta yi magana ne saboda wasu mutane na yaɗa bayanai a kafafen sada zumunta da ka iya haifar da rudani da tashin hankali.
Ya buƙaci jama’a su guji yada bayanan da ba a tabbatar da su ba, tare da barin kotu ta gudanar da aikinta yanzu da aka kai batun gabanta.




