CREDICORP: Za ku iya samun rance don sayen solar – Tinubu ya faɗa wa ’yan Najeriya

DA DUMI-DUMI

CREDICORP: Za ku iya samun rance don sayen solar – Tinubu ya faɗa wa ’yan Najeriya

Daga Wakiliya

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya ce ’yan Najeriya za su iya samun rance don sayen kayayyaki ta shirin CREDICORP, domin mallakar Solar, motoci da na’urorin zamani ba tare da sun jira sun tara kudade na tsawon shekaru ba.

Tinubu ya bayyana hakan ne a jawabinsa na bikin cikar Najeriya shekaru 66 da samun ’yancin kai.

Ya ce shirin na daga cikin matakan gwamnati na rage radadin tsadar rayuwa da kuma bai wa ’yan Najeriya damar samun muhimman kayayyaki da za su inganta rayuwarsu da sana’o’insu.

Shugaban ya kuma ce gwamnatin na tallafa wa daliban da iyayensu ba su da karfin biyan kudin karatu ta hanyar asusun lamunin karatu na NELFUND.

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

BRAZIL: Mutumin da matarsa ta yanke wa azzakari zai sake aurenta

Yanzu haka, Gilberto na shirin sake aurenta, inda zai yi amfani da kuɗin diyya da ya samu bayan an yaɗa hotunan raunukan da ya samu a intanet ba tare da izininsa na yaɗawa ba.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img