Shugaban APC ya tafi hutun mako biyu domin shirya wa zaɓen 2027

DA DUMI-DUMI

Shugaban APC ya tafi hutun mako biyu domin shirya wa zaɓen 2027

Daga Wakiliya

Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya tafi hutun mako biyu a ƙasar waje domin hutawa da sake tsara dabarun jam’iyyar gabanin zaɓen 2027.

A cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara kan yaɗa labarai, Abimbola Tooki, ya fitar, an ce hutun ya biyo bayan shafe shekara guda na ayyukan jam’iyya, tafiye-tafiye da shawarwari da shugaban ya gudanar.

Sanarwar ta ce Yilwatda zai kuma yi amfani da lokacin wajen tsara taron kwamitin gudanarwar jam’iyyar na ƙasa (NWC), wanda zai duba nasarorin da APC ta samu da kuma kalubalen da ke gabanta.

Sanarwar ta ƙara da cewa tafiyar shugaban ba za ta shafi ayyukan jam’iyyar ba, domin NWC na ci gaba da gudanar da harkokinta kamar yadda kundin tsarin APC ya tanada.

Ana sa ran shugaban zai dawo Najeriya bayan makonni biyu.

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

An kashe mutumin da ake zargi ya daba wa limamin Juma’a a Wuka a Sokoto

Rahotanni sun ce matashin, wanda aka bayyana da suna Mai Barewa, yana cikin masu ibadar da suka halarci sallar, kuma ya kai wa malamin hari har sau biyu.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img