Aliko Dangote Ya Yi Wasiyyar A Ware Kashi Ɗaya Bisa Uku Na Dukiyarsa Domin Ayyukan Jin Ƙai -inji Halima Dangote
Attajirin da ya fi kowa kuɗi a Afirka, Aliko Dangote, ya yi wasiyyar a ware kashi ɗaya bisa uku (33%) na dukiyarsa domin ayyukan jin ƙai da tallafa wa bil’adama, kamar yadda ‘yarsa Halima Dangote ta bayyana.
Halima, wacce ke cikin amintattun shugabannin Aliko Dangote Foundation, ta shaida wa Bloomberg cewa Dangote ya tsara wannan wasiyya tare da amincewar iyalansa domin tabbatar da cewa ayyukan jin ƙai za su ci gaba har bayan rayuwarsa.
Bisa ga Bloomberg Billionaires Index, an kiyasta dukiyar Dangote ta kai dala biliyan 35.1, wanda ke nufin kashi ɗaya bisa uku na wannan dukiya ya kai kusan dala biliyan 11.7, kwatankwacin Naira tiriliyan 16 idan aka mayar da ita kudin Najeriya.
Halima ta ce mahaifinta ya fi mayar da hankali wajen tallafawa fannonin lafiya da ilimi, tare da bayyana cewa tsarin ya yi daidai da tanadin Shari’ar Musulunci da ke ba mutum damar yin wasiyyar kashi ɗaya bisa uku na dukiyarsa.
Ta ƙara da cewa Dangote ya sanya ita, ‘yan’uwanta mata biyu da kuma mahaifiyarsa suka sanya hannu kan wasiyyar domin tabbatar da cewa wannan kaso na dukiyarsa zai ci gaba da amfani ga bil’adama.
An kafa Aliko Dangote Foundation a shekarar 1994, kuma gidauniyar na gudanar da ayyuka a fannonin lafiya, ilimi, abinci mai gina jiki da agajin jin ƙai a Najeriya da sauran ƙasashen Afirka. Har ila yau, ta yi haɗin gwiwa da Bill & Melinda Gates Foundation wajen yaƙi da cutar shan inna a Afirka.
A farkon wannan shekarar, mujallar TIME ta saka Aliko Dangote cikin jerin fitattun masu ayyukan jin ƙai na duniya (TIME100 Philanthropy), tana mai nuni da cewa yana kashe sama da Naira biliyan 50 a duk shekara wajen ayyukan alheri.





