2027: Akpabio ya musanta cewa ya ce ’yan Arewa za su sha wahala idan Tinubu ya fadi zabe

DA DUMI-DUMI

2027: Akpabio ya musanta cewa ya ce ’yan Arewa za su sha wahala idan Tinubu ya fadi zabe

Daga Wakiliya

Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Godswill Akpabio, ya musanta wata magana da ake yaɗawa a kafafen sada zumunta da aka danganta masa cewa ’yan Arewa za su fi shan wahala idan Shugaba Bola Tinubu ya fadi a zaɓen 2027.

Akpabio ya bayyana maganar a matsayin “ƙage ce tsagwaronta”, yana mai cewa babu bidiyo, sauti, jawabi ko wata sahihiyar hujja da ke nuna cewa ya taɓa furta kalaman.

Ya kuma ƙalubalanci waɗanda ke yaɗa maganar da su fito da cikakken bidiyo ko sauti da ke nuna inda, yaushe da kuma a gaban wa ya faɗi kalaman.

A wani mataki kuma, Akpabio ya kai ƙorafi ga DSS, inda ya nemi a binciki yadda aka ƙirƙiri tare da yaɗa hoton da ke ɗauke da kalaman da aka danganta masa.

Ya ce irin wannan magana na iya haddasa rikici da ƙiyayya tsakanin ’yan Arewa da Kudu, musamman yayin da ake tunkarar zaɓen 2027.

Akpabio ya ce siyasa ba ta kamata ta zama hanyar amfani da ƙabilanci wajen tayar da hankalin jama’a ba.

“Arewa ba makamin zaɓe ba ce. Kudu ba maƙiyi ba ce. Ƙabilanci ba makamin yaƙin neman zaɓe ba ne,” in ji shi.

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

Gwamnatin Najeriya za ta fara biyan tsoffin ma’aikatan Nigeria Airways Naira biliyan 18

Sai dai ya bayyana cewa gwamnati za ta biya kuɗin da aka tantance kuma aka tabbatar da shi, ba tare da ƙarin kuɗin da ya dace da hauhawar farashi na tsawon shekaru 20 ba.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img