Matsalar Najeriya ta samo asali ne daga rashin shugabanci nagari -Femi Adesina

DA DUMI-DUMI

Daga Wakiliya

Tsohon mai ba marigayi Shugaba Muhammadu Buhari shawara kan harkokin yaɗa labarai, Femi Adesina, ya ce babban abin da ke jawo tabarbarewar tattalin arziki da ci gaban Najeriya shi ne rashin shugabanci nagari.

Da yake jawabi a wani taron shekara-shekara da Foursquare Gospel Church ta shirya a jihar Oyo, Adesina ya ce Najeriya na da dimbin albarkatun ƙasa da na ɗan Adam, amma cin hanci da rashawa, rashin ingantaccen shugabanci, ƙarancin ababen more rayuwa da rashin aikin yi sun hana ƙasar cimma cikakken ci gabanta.

Ya ƙara da cewa shugabannin Najeriya tun daga zamanin Abubakar Tafawa Balewa har zuwa Shugaba Bola Ahmed Tinubu sun sha yin alƙawarin makoma mai kyau ga ƙasar, amma har yanzu alƙawuran ba su cika yadda ake fata ba.

Adesina ya buƙaci shugabanni su mayar da kalamansu zuwa aiki domin al’ummar Najeriya su amfana da albarkatun da ƙasar ta mallaka.

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

Gwamnatin Najeriya za ta fara biyan tsoffin ma’aikatan Nigeria Airways Naira biliyan 18

Sai dai ya bayyana cewa gwamnati za ta biya kuɗin da aka tantance kuma aka tabbatar da shi, ba tare da ƙarin kuɗin da ya dace da hauhawar farashi na tsawon shekaru 20 ba.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img