Yari ya ba ƙungiyarmu N550m don yaƙin neman zaɓen Tinubu, ya ce mu dawo idan bukatar ƙarin kuɗi ta taso – Rarara

DA DUMI-DUMI

Yari ya ba ƙungiyarmu N550m don yaƙin neman zaɓen Tinubu, ya ce mu dawo idan bukatar ƙarin kuɗi ta taso – Rarara

Fitaccen mawaƙin siyasar APC, Dauda Kahutu Rarara, ya ce tsohon gwamnan Jihar Zamfara kuma daraktan yaƙin neman zaɓen APC, Abdulaziz Yari, ya ba ƙungiyarsa ta Triple-R Naira miliyan 500 domin fara yaƙin neman zaɓen Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Rarara ya kuma ce Abdulaziz Yari ya ƙara ba ƙungiyar Naira miliyan 50 domin sayen man fetur da abinci yayin gudanar da ayyukan.

Rarara ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da BBC Hausa, inda aka tambaye shi kan zargin cewa yana karɓar makudan kuɗaɗe daga ’yan siyasa da sunan ƙungiyar, ba tare da raba wa mambobinta abin da ya kamata ba.

Da yake bayani kan N500m ɗin, Rarara ya ce an ba su kuɗin ne domin su fara ayyukan yaƙin neman zaɓen Bola Ahmed Tinubu.

“Akwai wannan N500m, ya amince zai ba mu kuɗi mu fara wannan harkar yaƙin neman zaɓen Bola Ahmed Tinubu. Bayan N500m ɗin, ya ba mu N50m ya ce na man fetur da abinci ne,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa sauran N500m ɗin an ba su ne domin fara gudanar da ayyukan da suka shafi yaƙin neman zaɓen, kuma daga baya an ce su gabatar da kasafin kuɗin da suke buƙata idan an kammala ayyukan farko.

Da aka tambaye shi game da adadin kuɗin da Yari ya ba su da lokacin da zai raba kuɗin gudanarwa ga mambobin ƙungiyar, Rarara ya ƙi yin cikakken bayani.

“Me ya sa zan bayyana maka? Shin jama’a ne suka aiko ka ka bincika wannan?” in ji shi.

Rarara ya ce ƙungiyar tana aiki ne bisa wasu ƙa’idoji, yana mai cewa kuɗin da aka ba su an ware su ne domin gudanar da ayyukan.

“Idan za mu yi tafiya, ba za mu ci abinci ba? Ba za mu sauka a otal ba? Ba za mu sa mai a mota ba? N50m ɗin na man fetur da abinci ne, N500m kuma na aikin da muka yi ne,” in ji shi.

‘Masu zarginmu kuɗi suke nema’

Rarara ya kuma yi watsi da zargin wasu daga cikin mambobin ƙungiyar da ke cewa ana amfani da su wajen karɓar kuɗaɗe daga ’yan siyasa ba tare da an ba su rabonsu ba.

Ya ce mutanen da ke yin irin wannan zargi suna neman kuɗi ne kawai.

“Duk wanda yake kawo irin waɗannan maganganu, kuɗi yake nema,” in ji Rarara.

Rarara ya kare manufofin Tinubu

A cikin hirar, Rarara ya kuma kare manufofin tattalin arzikin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, duk da korafe-korafen ’yan Najeriya kan tsadar rayuwa da hauhawar farashin man fetur.

Ya ce ya yi imanin cewa Tinubu ba ya yaudarar ’yan Najeriya, kuma gyaran da yake yi zai ɗauki lokaci kafin a fara ganin cikakken sakamakonsa.

“Tinubu ba ya ƙarya ko yaudara; yana gyara ƙasar nan. Idan ba mu gyara ta yanzu ba, wani mutum nan gaba zai gyara ta, ko kuma ƙasar ta rushe,” in ji shi.

Game da farashin man fetur da ya haura N1,500 a wasu sassan ƙasar, Rarara ya ce ba shi da cikakken ilimin fasaha kan harkokin NNPCL da masana’antar mai.

Sai dai ya ce abubuwan da ke faruwa a duniya, ciki har da rikicin Iran, na iya yin tasiri kan farashin makamashi.

Ya ce bai ce man fetur yana da arha a ko’ina ba, amma a ganinsa har yanzu farashin man fetur a Najeriya yana cikin wadanda ba su kai na wasu ƙasashe ba.

Rarara ya kwatanta halin da tattalin arzikin Najeriya ke ciki da mutum mai karayar ƙafa, yana mai cewa ba za a sa ran mutum ya fara gudu nan take bayan an gyara masa ƙafarsa ba.

Ya ce ana buƙatar haƙuri yayin da ake aiwatar da sauye-sauyen tattalin arziki.

Rarara ya ƙara da cewa daga cikin wasu muhimman kayan abinci, an samu sauƙi a farashin wasu, yayin da ake ci gaba da ƙoƙarin rage farashin sauran.

Ya kuma ce ana sa ran farashin takin zamani zai ragu nan gaba.

A cewarsa, hangen nesan Shugaba Tinubu ba wai na yau ko gobe kawai ba ne, illa dai na shekaru 10 zuwa 20 masu zuwa.

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

’Yan Najeriya Haƙuri Kawai Suke Yi, Ba Sa Jin Daɗin Gwamnatinka – Wahalar Ta Yi Yawa – Dattawan Kiristocin Arewa sun gargadi Tinubu

Ta ƙara da cewa gwamnati ta nemi wasu hanyoyin samun kuɗaɗen shiga masu ɗorewa, maimakon ci gaba da ɗora nauyin ƙarin kuɗin man fetur kan jama’a (Talakawa).
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img