Akalla mutum 30 sun mutu a hannun jami’an Civil Defence (NSCDC) a jihar Niger

DA DUMI-DUMI

RAHOTON: Akalla mutum 30 sun mutu a hannun jami’an Civil Defence (NSCDC) a jihar Niger

Daga Wakiliya

Hukumar NSCDC ta Jihar Neja ta ce wasu daga cikin mutanen da take tsare da su bisa zargin haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba sun mutu sakamakon abin da ake zargin ɓarkewar cuta. Kimanin yara matasa 30 aka nuna gawarwakinsu a wani bidiyo.

A cikin wata sanarwa da Kwamandan hukumar, Suberu Siyaka Aniviye, ya fitar, ya ce an kama mutanen ne a ranakun 15 da 16 ga Satumba, yayin samamen da aka kai wuraren haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba a MI Wushishi Estate da ƙauyen Lukoto da ke Minna.

Sanarwar ta ce an kai gawarwakin waɗanda suka mutu Babban Asibitin Minna domin gudanar da bincike na likitoci don gano ainihin abin da ya haddasa mutuwar.

Hukumar ta buƙaci jama’a da iyalan mamatan su kwantar da hankula, tana mai cewa tana aiki tare da sauran hukumomin tsaro don shawo kan lamarin.

Me ya kamata ayi?

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

’Yan Najeriya Haƙuri Kawai Suke Yi, Ba Sa Jin Daɗin Gwamnatinka – Wahalar Ta Yi Yawa – Dattawan Kiristocin Arewa sun gargadi Tinubu

Ta ƙara da cewa gwamnati ta nemi wasu hanyoyin samun kuɗaɗen shiga masu ɗorewa, maimakon ci gaba da ɗora nauyin ƙarin kuɗin man fetur kan jama’a (Talakawa).
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img