’Yan Najeriya Haƙuri Kawai Suke Yi, Ba Sa Jin Daɗin Gwamnatinka – Wahalar Ta Yi Yawa – Dattawan Kiristocin Arewa sun gargadi Tinubu

DA DUMI-DUMI

’Yan Najeriya Haƙuri Kawai Suke Yi, Ba Sa Jin Daɗin Gwamnatinka — Wahalar Ta Yi Yawa – Dattawan Kiristocin Arewa sun gargadi Tinubu

Daga Wakiliya

Ƙungiyar Dattawan Kiristocin Jihohin Arewa ta gargaɗi Shugaba Bola Tinubu da kada ya ɗauki haƙurin ’yan Najeriya a matsayin amincewa da tsananin wahalhalun da suke ciki.

A cikin wata sanarwa da shugaban ƙungiyar, Elder Sunday Oibe, ya fitar ranar Alhamis, ƙungiyar ta buƙaci gwamnati ta janye sabon ƙarin farashin man fetur.

Ta ce ƙarin farashin zai ƙara tsananta matsin tattalin arziki da kuma rashin tabbas da miliyoyin ’yan Najeriya ke fuskanta.

Ƙungiyar ta kuma yi kira ga Shugaba Tinubu da ya mayar da hankali kan rage tsadar rayuwa, rashin aikin yi, rashin tsaro da kuma gyaran muhimman ababen more rayuwa.

“Bai kamata a ɗauki haƙurin ’yan Najeriya a matsayin amincewa da wahala marar iyaka ba,” in ji ƙungiyar.

Ta ƙara da cewa gwamnati ta nemi wasu hanyoyin samun kuɗaɗen shiga masu ɗorewa, maimakon ci gaba da ɗora nauyin ƙarin kuɗin man fetur kan jama’a (Talakawa).

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

Akalla mutum 30 sun mutu a hannun jami’an Civil Defence (NSCDC) a jihar Niger

Akalla mutum 30 sun mutu a hannun jami'an Civil Defence (NSCDC) a jihar Niger
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img