Gwamnonin APC Ba Su Ji Daɗi Da Na Zama Ministan Abuja Ba – Muƙamina ya tsokane masu ido -Wike
Daga Wakiliya
Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya zargi gwamnonin jam’iyyar APC da rashin jin daɗin kasancewarsa Ministan Babban Birnin Tarayyar Abuja, FCT.
Wike ya bayyana hakan ne a wata hira da aka yi da shi ranar Talata, yayin da yake magana kan adawar da wasu gwamnonin APC ke yi wa haɗin gwiwar Rainbow Coalition a Jihar Rivers.
Ministan ya kuma zargi gwamnonin APC da yaudarar Gwamna Siminalayi Fubara a lokacin rikicin siyasar jihar, yana mai cewa sun kasa tabbatar masa da wa’adi na biyu.
“Ba su ji daɗin cewa an ba ni Ministan FCT ba,” in ji Wike.
Ya ƙara da cewa kasancewar mutum gwamna ba ya nufin duk abin da ya yanke dole ne ya faru ba, yana mai cewa shi ma ya taɓa kayar da ɗan takarar gwamnan da ke kan mulki a zaɓen 2015, a lokacin da yake Ministan Ƙasa.




