Matar El-Rufai ta zargi gwamnatin Tinubu da yi wa El-Rufai bita da ƙullin siyasa
Daga Wakiliya
Matar tsohon gwamnan Kaduna, Asia El-Rufai, ta zargi gwamnatin tarayya a ƙarƙashin Shugaba Tinubu da tsare mijinta na dogon lokaci da kuma gudanar da bincike a kansa bisa dalilan siyasa.
Asia, wadda lauya ce, ta bayyana hakan a cikin wani shirin bidiyo da ƙungiyar Justice For El-Rufai Project ta fitar.
Ta ce ba a zargi mijinta da wani laifi ba a lokacin da yake cikin jam’iyyar APC, sai dai an fara yi masa zarge-zarge da barazana ne biyan ficewarsa daga jam’iyyar APC zuwa SDP zuwa ADC.
Asia ta kuma ce El-Rufai ya musanta dukkan zarge-zargen da ake yi masa a gaban kotuna uku, tare da neman beli.
Ta ce laifukan da ake tuhumarsa da su na da damar beli, tana mai cewa: “Beli hakki ne, ba gata ba.”
Don haka suna ɗaukar tsare tsohon gwamnan a matsayin bita da ƙullin siyasa.




