Wakiliya Ta Bude Kafarta Ga Masu Fafutukar “Tinubu Must Go”, Za Ta Wallafa Sakonsu Kyauta

DA DUMI-DUMI

Wakiliya Ta Bude Kafarta Ga Masu Fafutukar “Tinubu Must Go”, Za Ta Wallafa Sakonsu Kyauta

Daga Wakiliya

Sabuwar kafar yada labarai ta Wakiliya ta bayyana matsayarta kan halin da Najeriya ke ciki, inda ta sanar da cewa daga yanzu za ta ba masu fafutukar “Tinubu Must Go” (TMG) damar yada sakonsu kyauta a kafarta.

Wakiliya ta kuma ce za ta karkatar da akalar shirye-shiryenta zuwa bincike da nazarin abubuwan da suka faru a baya, halin da ake ciki yanzu da kuma abubuwan da ka iya faruwa nan gaba, domin fito da hujjoji da dalilan neman sauyin gwamnati a 2027.

Sanarwar na zuwa ne a daidai lokacin da ‘yan Najeriya, musamman al’ummar Arewa, ke ci gaba da fuskantar matsalolin tsaro, kashe-kashe, garkuwa da mutane da kuma matsin rayuwa.

Daga cikin abubuwan da suka kara jawo hankalin jama’a a baya-bayan nan akwai mutuwar mutane 37 da ke tsare a hannun NSCDC a Minna, Jihar Neja, lamarin da ya sa aka fara bincike domin gano abin da ya haddasa mutuwar.

Wakiliya ta ce duba da irin wadannan abubuwa da sauran matsalolin da jama’a ke fuskanta, ta ga ya dace ta ba masu fafutukar “Tinubu Must Go” damar isar da sakonsu ga jama’a kyauta.

Duk wani rubutu, bidiyo, sharhi, rahoto, tsokaci, ko wani nau’in tattaunawa da ya dace da ka’idojin wallafawa, wanda ke da alaka da wannan kira ko bayyana matsalolin da ‘yan Najeriya ke fuskanta, Wakiliya za ta wallafa shi kyauta, muddin ya cika ka’idojin wallafawa.

Haka kuma, Wakiliya ta ce shirye-shiryenta da podcasts dinta za su mayar da hankali wajen zurafa bincike da tattaunawa kan manufofi, ayyuka da sakamakon manufofin gwamnati, tare da gabatar da hujjoji da ra’ayoyi daban-daban da suka shafi makomar Najeriya da kuma kiran “Tinubu Must Go.”

 

Wakiliya ta ce:

“Kowa na da tasa gudunmawar da zai bayar wajen ganin an samu sauyi mai kyau a Najeriya. Wannan shi ne namu gudunmawar wajen ganin an yi abin da ya dace, tare da zaburar da shugabanni su yi abin da ya dace ga jama’arsu da kasar nan, musamman yankin Arewacin Najeriya.”

Kafar ta kara da cewa za ta ci gaba da bai wa matsalolin da suka shafi Arewa da sauran sassan Najeriya muhimmiyar dama a kafarta.

A karshe, Wakiliya ta jajantawa iyalan wadanda suka rasa rayukansu da kuma daukacin ‘yan Najeriya, musamman al’ummar Arewacin Najeriya, kan matsin rayuwa, rashin tsaro da asarar rayuka da dukiyoyi.

Wakiliya ta kuma yi kira ga gwamnati da hukumomin tsaro da su dauki matakin gaggawa wajen kubutar da ‘yan Najeriya da ke hannun masu garkuwa da mutane, tare da kara kokarin kare rayuka da dukiyoyin jama’a.

Wakiliya ta ce za ta ci gaba da wannan matsaya har sai an samu matakan da za su magance matsalolin da jama’a ke fuskanta.

 

Wannan ba labari kawai ba ne.

MURYAR JAMA’A CE.

MURYAR AREWA CE.

WAKILIYA CE.

 

Wakiliya – Muryar Arewa a Duniya.

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

Yari ya ba ƙungiyarmu N550m don yaƙin neman zaɓen Tinubu, ya ce mu dawo idan bukatar ƙarin kuɗi ta taso – Rarara

A cewarsa, hangen nesan Shugaba Tinubu ba wai na yau ko gobe kawai ba ne, illa dai na shekaru 10 zuwa 20 masu zuwa.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img