Elon Musk ya kuma yi magana kan lokacin da AI za ta zarce basirar ɗan Adam, saurin ci gaban fasaha a ƙasar Sin, dalilan da suka sa yake ƙara mayar da hankali kan Turai, da kuma rawar da ya taka a siyasa, inda ya amince cewa ya "ɗan tsunduma cikin harkokin siyasa fiye da yadda ya kamata."
Masana sun bayyana cewa duk da iPhone 17 na ci gaba da yin suna wajen ɗaukar bidiyo da sauƙin amfani da kyamara, wayoyin Android na zamani sun rage tazarar da ke tsakaninsu, kuma wasu ma sun zarce ta a fannoni kamar zoom, hotunan dare da kuma manyan na'urorin kyamara.
FCCPC ta tuna cewa a baya ta ci shari'a kan Meta kan wasu laifuffuka da suka shafi dokar kare masu amfani, inda aka ci tarar kamfanin dala miliyan 220, duk da cewa har yanzu kamfanin ya ɗaukaka ƙara.