Zan so na rika fitowa a budurwa maimakon uwa a fim -in ji Rahama Sidi

Zan so na rika fitowa a budurwa maimakon uwa a fim -in ji Rahama Sidi

Daga Wakiliya

Fitacciyar jarumar Kannywood, Rahama Sidi Aliyu, ta ce tana son ta rika fitowa a matsayin budurwa a fina-finai maimakon matsayin uwa, saboda a cewarta ba ta kai shekarun da za a rika saka ta a irin wannan matsayi ba.

Rahama Sidi ta bayyana hakan ne yayin wata hira da tashar Fact News, inda ta ce ta kwashe kusan shekara takwas tana harkar fim, kuma fim din farko da ta fara yi shi ne Farar Mace na Abubakar Dan Sudan.

Jarumar ta ce daga cikin fina-finan da ba za ta taba mantawa da su ba akwai fim din Labari na, wanda ta bayyana cewa yana da muhimmanci a rayuwarta ta sana’ar fim.

Ta kuma yi magana kan wata matsala da ta taba fuskanta bayan wata hira da ta yi da BBC, inda ta ce an samu rashin fahimta bayan ta bayyana cewa iyayenta ‘yan Ghana ne. Ta ce ba haka lamarin yake ba, domin asalinsu ‘yan Kano ne, sai dai fatauci ya kai su Ghana.

Rahama Sidi ta ce harkar fim ta taimaka mata wajen cimma wasu nasarori a rayuwa, ciki har da mallakar mota da gida nata, tare da wasu abubuwa da dama da ta samu ta hanyar sana’ar.

Ta musanta jita-jitar cewa ta taba auren wani dan fim, inda ta ce abin da ya faru shi ne ta auri dan wani fitaccen jarumi ne, Kasimu Yaro.

Jarumar ta ce babban burinta a gaba shi ne ta zama babbar furodusa a masana’antar shirya fina-finai.

DA DUMI-DUMI

ICPC ta gano jami’in da ya saka ‘yan uwansa 14 a albashin gwamnati, da kuma mai karbar albashi 13 shi kadai

Musa Aliyu ya ce hukumar za ta kara amfani da fasaha da bayanai wajen dakile cin hanci da kare dukiyar gwamnati, tare da mayar da hankali kan hana barna kafin faruwar ta.

Beli kyauta ne’ Idan aka nemi ku bayar da kudi, ku kira IGP’ — Rundunar ‘yan Sandan Najeriya

“Doka ba ta ba da damar wani ya biya kudi domin beli ba a kowane ofishin ‘yan sanda a Najeriya,” in ji shi.

Matatun man fetur din Najeriya za su dawo aiki – Tinubu

“Na karbi dukkan nauyin da ya shafi abin da ya faru a baya. Nauyin da ke kaina yanzu shi ne gyara tattalin arziki domin amfanin mafi yawan ‘yan Najeriya,” in ji shugaban.

Dan siyasar da ya rantse da Alƙur’ani zai ci gaba da biyayya ga Kwankwaso ya koma APC

Ya ce ya ɗauki matakin ne sakamakon abin da ya kira rashin cika alkawura daga jam’iyyar, yana mai cewa yanzu zai mara wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu baya a zaɓen 2027 a ƙarƙashin APC.

Musulmi da Kiristoci sun rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a Abuja

Sun kuma jaddada cewa manufar yarjejeniyar ba wai hada addinai wuri daya ba ce, sai dai gina fahimtar juna da girmama bambance-bambance.

Kanun Labarai

Ana tsare da El-Rufai ne saboda ya raba gari da Tinubu – Mataimakin Atiku – M/Atiku

Ya ce, “Wace irin shaida ake bukata don tabbatar da cewa ana yakar ‘yan adawa ne ba cin hanci da rashawa ba?”

Matar da ta shafe shekaru tana ƙaurace wa nama sai ganyayyaki ta fashe da kuka bayan ta ci nama karo na farko

Soo a wani dogon bidiyo ta bayyana cewa dalilin da ya sa ta fara cin abinci marar nama ba wai kawai saboda kare dabbobi ko muhalli ba ne. Ta bayyana cewa tsawon shekaru tana kokarin rage kiba, kuma daga bisani tsarin vegan ya koma wani nau'in takura wa kanta wajen cin abinci saboda yadda take kallon jikinta.

Wayoyi biyar da aka kera a China da za su iya fafatawa da Galaxy S26

Wayoyi biyar da aka kera a China da za su iya fafatawa da Galaxy S26Matsalar Rashin Yarda Da Ke Hana Kasuwancin Intanet Bunƙasa a Najeriya Daga Wakiliya Kasuwancin intanet na ci gaba da bunƙasa a Najeriya. Kowace rana, miliyoyin mutane na saye da sayarwa ta shafukan sada zumunta kamar WhatsApp, Facebook, Instagram da sauran dandamalin kasuwanci. Sai dai duk da wannan ci gaba, akwai wata babbar matsala da ke hana kasuwancin ya kai matsayin da ake sa ran zai kai — rashin amincewa tsakanin mai saye da mai sayarwa. "Me zai hana idan aka damfare ni?" Wannan ita ce tambayar da mafi yawan 'yan Najeriya ke yi kafin su tura kuɗi ga wani da ba su taɓa hulɗa da shi ba. An sha samun labaran mutane da aka yaudara bayan sun biya kuɗin kaya amma ba a aiko musu da komai ba. Haka kuma akwai masu sayarwa da suka tura kaya amma ba a biya su kuɗinsu ba. Saboda haka, kowanne ɓangare yana jin tsoron shi ne zai fara ɗaukar haɗari. Matsalar ba ta biyan kuɗi ba ce, matsalar ita ce amana A yau, aika kuɗi ta banki ko manhajojin kuɗi ya zama abu mai sauƙi a Najeriya. Amma sauƙin tura kuɗi ba yana nufin an magance matsalar kasuwanci ba. Babbar matsalar ita ce yadda za a tabbatar cewa: - Mai saye zai karɓi kayan da ya biya. - Mai sayarwa kuma zai samu kuɗinsa bayan ya aika da kaya. Idan babu tabbacin hakan, mutane da dama kan fasa cinikin gaba ɗaya. Illolin rashin amincewa Masana sun ce wannan matsala na rage bunƙasar kasuwancin intanet ta hanyoyi da dama: - Masu saye na fasa sayayya saboda tsoron damfara. - Masu sayarwa na rasa kwastomomi. - Sabbin 'yan kasuwa na wahalar samun amincewar jama'a. - Mutane na takaita kasuwanci ga waɗanda suka sani kawai, maimakon faɗaɗa zuwa sababbin kwastomomi. Wannan na rage yawan ciniki da kuɗaɗen da za su riƙa zagayawa a tattalin arziki. Hanyoyin da ake amfani da su ba su wadatar ba Akwai hanyoyi daban-daban da ake ƙoƙarin magance matsalar, kamar: - Biyan kuɗi bayan an kawo kaya. - Duba ra'ayoyin kwastomomi (reviews). - Yin ciniki da mutanen da aka sani kawai. Sai dai kowacce hanya na da matsalolinta. Wasu suna ƙara tsada, wasu kuma ana iya yin magudi da su. Mene ne mafita? Masana harkar kasuwancin intanet sun ce abin da ake buƙata shi ne samar da tsarin da zai kare bangarorin biyu. Daga cikin hanyoyin da ake ba da shawara akwai: - Yin amfani da amintattun hanyoyin biyan kuɗi masu ba da kariya ga mai saye da mai sayarwa. - Amfani da tsarin escrow, inda wani amintaccen ɓangare ke riƙe kuɗin ciniki har sai an tabbatar an kammala cinikin yadda ya kamata. - Tabbatar da sahihancin bayanan masu ciniki (identity verification). - Ƙarfafa dokoki da matakan kare masu amfani da harkar kasuwancin intanet. - Ilimantar da jama'a kan yadda za su guji damfara ta yanar gizo. Me hakan zai haifar? Idan aka samu ingantaccen tsarin da zai ƙarfafa amincewa: - Sabbin 'yan kasuwa za su samu damar yin gogayya cikin sauƙi. - Masu saye za su riƙa ciniki ba tare da fargaba ba. - Kasuwanci zai bunƙasa tsakanin mutane ko da ba su san juna ba. - Tattalin arzikin dijital na Najeriya zai ƙara girma. Kasuwancin intanet ba ya rasa masu saye ko masu sayarwa a Najeriya. Abin da yake buƙata shi ne tsarin da zai tabbatar wa kowa cewa kuɗinsa da kayansa suna cikin aminci. Idan aka magance matsalar rashin amincewa, hakan zai buɗe ƙofar samun ci gaba mai yawa ga kasuwancin intanet a kasar.
spot_img

Labarai masu alaka

Sauran bangarori

spot_imgspot_img