Dino Melaye ya shawarci Tinubu da iyalansa su fara tattara kayansu daga Villa – Don za APC za ta sha kaye a 2027
Daga Wakiliya
Ɗan siyasa kuma jigo a jam’iyyar ADC, Sanata Dino Melaye, ya ce Shugaba Bola Ahmed Tinubu da iyalansa su fara shirin barin Fadar Shugaban Ƙasa kafin zaɓen 2027.
Melaye ya bayyana cewa ADC za ta kayar da jam’iyyar APC a zaɓen, yana mai cewa sakamakon zai nuna rashin gamsuwar al’ummar Najeriya da halin yunwa, rashin tsaro da kuma yadda ya ce ake tafiyar da gwamnati.
Da yake magana a gidan talabijin na Arise TV ranar Litinin, tsohon sanatan ya ce dabarar ADC ta lashe zaɓen ba ta da wahala, domin a cewarsa, “al’umma suna tare da mu.”
Ya zargi gwamnatin Tinubu da gazawar aiwatar da kasafin kuɗi, yana mai cewa an ci gaba da karɓar bashi ba tare da aiwatar da kasafin kuɗin yadda ya kamata ba.
Ya kuma yi iƙirarin cewa wasu kwangilolin da aka bayar tun 2024 har yanzu ba a biya kuɗinsu ba, yayin da gwamnati ke ci gaba da aiwatar da kasafin kuɗin shekarar 2024 a cikin 2026.
Melaye ya ce matsalolin yunwa, kashe-kashe da sata sun nuna cewa akwai babban gibi tsakanin gwamnati da al’ummar ƙasar.
Ya kuma zargi Shugaba Tinubu da kuma jam’iyyarsa da mayar da magudin zaɓe, tashin hankali da satar ƙuri’u wani abu da ake ɗauka a matsayin al’ada a siyasa.
“Ina gaya muku, sakamakon zai bayyana a watan Janairu. Shugaban ƙasa da iyalansa su fara tattara kayansu daga Villa, har da waɗanda ke cikin gidan ma’aikata, domin za a samu sauyin gwamnati,” in ji Melaye.




