Tun kafin Aurenmu nasan ba zai yi ƙarko ba – Halima tsohuwar matar Bashir El-Rufai ta yi magana kan rayuwarta bayan rabuwar aurensu

Halima tsohuwar matar Bashir El-Rufai ta yi magana kan rayuwarta bayan rabuwar aurensu

Daga Wakiliya

Halima Nwakego, tsohuwar matar Bashir El-Rufai, ta yi magana kan rayuwarta bayan rabuwar aurensu, da yadda take renon ’ya’yanta tagwaye.

Bashir, ɗan tsohon gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai, ya auri Halima, ’yar tsohon Sanatan Jigawa Ibrahim Kazaure, a shekarar 2020.

Sun haifi ’ya’ya tagwaye maza biyu a shekarar 2021.

A watan Yulin 2024 ne aurensu ya ƙare.

Bashir ya sanar da rabuwar a lokacin, inda ya yi amfani da kalmar “Gen Z wahala”. Daga baya ya nemi afuwa kan yadda ya sanar da batun.

A wani rubutu da ta wallafa, Halima ta ce tun kafin ta yi aure ba ta da cikakken yakinin cewa aurenta zai daɗe.

Ta ce har tana ganin kamar aurenta zai ƙare tun kafin ya fara.

“Na shiga aure ne ina tunanin yadda zai ƙare,” in ji ta.

Halima ta ce bayan rabuwar, ta sake soyayya da wani mutum, amma dangantakar ta ƙare da ɓacin rai.

Ta ce duk da cewa ba ta da cikakken amincewa da maza, tana da babban imani da soyayya.

“Ga wanda ba shi da cikakken imani da maza kamar ni, ina da matuƙar imani da soyayya,” in ji ta.

Halima ta kuma yi magana kan rayuwarta a matsayin uwa mai renon ’ya’ya ita kaɗai, kasuwancinta da kuma rayuwa da ADHD, wato matsalar rashin iya mai da hankali na dogon lokaci.

DA DUMI-DUMI

Me ya sa za ku saka duk wanda kuka taɓa magana da shi sau ɗaya ko biyu a WhatsApp Group ɗin aurenku? – Mr....

Mr. Abdul Reacts ya ce matasan Najeriya da dama kan taimaka wa akalla biki ɗaya kusan kowane wata, ko da kuwa ba su da hali, abin da ya kwatanta da wani nau'in “haraji” da ake biya saboda kasancewa cikin abokan hulɗa.

Bai kamata addini ya zama ma’aunin zaɓe a Najeriya ba domin a tsarin dimokuraɗiyya, tikitin Musulmi da Musulmi, Kirista da Kirista, Musulmi da Kirista...

Ya ce da a ce Najeriya tana tafiyar da mulkin Shari’a yadda Alƙur’ani da koyarwar Annabi Muhammad (SAW) suka tanada, to Musulmi ne kaɗai za su iya neman shugabanci.

Tinubu ya bai wa Famadewa ragamar tsara sabon tsarin tsaron Najeriya na shekaru biyar

Shugaban ya ba kwamitin kwanaki 90 domin kammala aikin da gabatar da shi gare shi domin amincewa.

An cire wa wani mutum dutse mai nauyin kilogiram 3.1 daga mafitsararsa a Sri Lanka

Duwatsu a mafitsara na samuwa ne lokacin da fitsari ya dade yana zama a cikin mafitsara, lamarin da ke sa wasu sinadarai da ke cikinsa su taru su zama dutse.

Dukan yara a matsayin horo na iya sa su fanɗare su zama mugaye idan sun girma -inji Masana

Ta ce saboda haka, horon da ya fi mayar da hankali kan fahimtar kuskure da koyar da yaro abin da ya dace na iya zama mafi amfani fiye da hukuncin da ke jawo tsoro kawai.

Kanun Labarai

Matashi ya yi bidiyo a TikTok ya yi ‘tagging’ Shugaban New York, yana korafi a gyara wasu ramuka da ya gani – kafin ya...

Matashi ya yi bidiyo a TikTok ya yi 'tagging' Shugaban New York Mamdani, yana korafi a gyara wasu manyan ramuka da ya gani – kafin ya je aiki ya dawo har an gyara

Kocin Masar ya suma yayin da yake ƙoƙarin raba faɗa tsakanin matansa, daga bisani ya saki uwargidarsa

Hossam Hassan, tsohon ɗan wasan tawagar ƙasar Masar ne kuma wanda ya fi kowa cin ƙwallaye a tarihin ƙasar. Ya fara horar da tawagar ƙasar a shekarar 2024.

Da kyar Tinubu ya amince da Osinbajo a matsayin mataimakin Buhari – ya dage sai an bai wa matarsa Oluremi

Atiku ya bayyana hakan ne a wata hira, inda ya kuma ce lokacin da Buhari ya nemi goyon bayansa bayan taron APC na 2014, ya sharɗanta masa cewa kada ya tsaya da tikitin Musulmi da Musulmi.
spot_img

Labarai masu alaka

Sauran bangarori

spot_imgspot_img