NELFUND: Mun raba wa ɗalibai miliyan 1.2 Naira biliyan 322 -Gwamnatin Tarayya
Daga Wakiliya
Gwamnatin Tarayya ta ce ta raba Naira biliyan 322 ga ɗalibai miliyan 1.2 a matsayin bashin karatu da tallafin kuɗin masauki, ƙarƙashin Asusun Ba da Lamunin Ilimi na Najeriya (NELFUND).
Ministan Ilimi, , ne ya bayyana hakan, inda ya ce adadin kuɗin ya kai haka ne zuwa ranar 8 ga watan Agusta.
Ministan ya kuma ce gwamnati na shirin sake duba dokokin da suka shafi kuɗaɗen riba da ba a karɓa ba da kuma kuɗaɗen da ke cikin asusun banki da ba a amfani da su, domin duba yiwuwar a yi amfani da wani ɓangare na kuɗaɗen wajen tallafa wa NELFUND.
Ya ce hakan na da nasaba da umarnin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na cewa a yi amfani da kuɗaɗen da Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) ta kwato ne kawai idan an tabbatar da cewa ba su da wata matsalar shari'a.
A cewar ministan, ana yin wannan bitar ne domin tabbatar da cewa duk wani kuɗi da za a tura wa NELFUND bai shiga wata ƙara ko takaddama ta shari'a ba.
Ya ce Attorney-General kuma Ministan Shari'a, Lateef Fagbemi (SAN), tare da shi da Ministan Kuɗi, Taiwo Oyedele, da sauran hukumomin da abin ya shafa, an umarce su da su tsara yadda za a aiwatar da umarnin.
Ministan ya ce za a duba dokokin da suka kafa Asusun Amana na Kuɗaɗen Ribar Hannun Jari da ba a karɓa ba da kuma Asusun Amana na Kuɗaɗen Dormant Accounts, domin tabbatar da cewa duk wani mataki da za a ɗauka ya dace da doka.
Shugaba Tinubu ya ce ana buƙatar NELFUND ya kasance mai isasshen kuɗi kuma mai ɗorewa domin ci gaba da biyan buƙatun ɗaliban Najeriya.





