Adam A. Zango ya sake aure a Jamhuriyar Nijar – Ya Auri Mamah
Daga Wakiliya
Fitaccen jarumin fina-finan Kannywood, Adam A. Zango, ya sake yin aure a Jamhuriyar Nijar.
An ɗaura sabon auren Jarumin ne a ranar Juma’a, 14 ga watan Agustan 2026, inda ya ce ya yi hakan ne da fatan samun dacewa da wannan lokaci na watan Rabi’ul Awwal.
A wani bidiyo da ya wallafa bayan bikin, Adam A. Zango ya gode wa Allah bisa kammala bikin, tare da neman addu’ar masoya da magoya bayansa domin samun zaman lafiya da dorewar auren.
Martani ga masu suka
Jarumin ya kuma mayar da martani ga mutanen da ke sukar sabon auren nasa.
Ya ce bai taɓa shiga aure da niyyar rabuwa da matar da ya aura ba, yana mai cewa rabuwar da ta faru a auren da ya gabata ƙaddara ce.
“Ba na shiga aure da niyyar zan rabu da matar. Abin da ya faru a baya ƙaddara ce,” in ji shi.
Adam A. Zango ya ce abin da ya fi nema a yanzu shi ne samun kwanciyar hankali da zaman lafiya a sabon gidansa.
Ya kuma roƙi masoyansa da su ci gaba da yi masa addu’a domin Allah Ya ba shi zaman lafiya, Ya kuma sa sabon auren ya dore.
Sabon auren na zuwa ne bayan rabuwar da jarumin ya yi da matar da ya aura a baya, lamarin da ya janyo ce-ce-ku-ce daga wasu daga cikin masoya da masu bibiyar rayuwarsa.




