Gwamnatin Tarayya za ta sake duba tallafin karatu a ƙasashen waje

Gwamnatin Tarayya za ta sake duba tallafin karatu a ƙasashen waje

Daga Wakiliya

Gwamnatin Tarayya ta ce tana sake duba tsarin tallafin karatu da yarjejeniyoyin ilimi da take da su da wasu ƙasashen waje, domin rage kashe kuɗin gwamnati da kuma mayar da hankali wajen ƙarfafa manyan makarantun Najeriya.

Ministan Ilimi, Dokta Tunji Alausa, ya ce gwamnati ba za ta ci gaba da kashe kuɗin jama'a wajen tura ɗalibai ƙasashen waje domin karatun darussan da ake koyarwa a jami'o'i, kwalejojin ilimi da kwalejojin fasaha na Najeriya ba.

Ministan ya bayyana hakan ne yayin da yake bayani kan dalilin da ya sa gwamnati ta sake duba tsarin tallafin karatun da ake bai wa ɗalibai a ƙasashen waje.

Ya ce matakin na daga cikin ƙoƙarin gwamnati na gina ƙwarewar cikin gida da kuma tabbatar da cewa ana amfani da kuɗin jama'a yadda ya kamata.

Dokta Alausa ya ce jim kaɗan bayan ya fara aiki a ma'aikatar, an gabatar masa da wani shiri da ya tanadi tura kusan ɗaliban Najeriya 100,000 zuwa Morocco domin karatun wasu darussa da ake koyarwa da Turanci, ciki har da aikin jarida da sadarwa.

Sai dai ya ce abin ya ba shi mamaki, saboda ana koyar da irin waɗannan darussa a Najeriya, yayin da ɗaliban kuma za su fara da koyon harshen Faransanci na tsawon shekara guda kafin su fara karatun fannonin da suka je yi.

Ya ce: “Na farko, muna da duk waɗannan darussan a Najeriya. Na biyu kuma, za su shafe shekararsu ta farko suna koyon Faransanci kafin su fara karatun.”

Ministan ya ƙara da cewa, maimakon gwamnati ta kashe makudan kuɗaɗe wajen tallafa wa ɗalibai a ƙasashen waje, za ta iya amfani da kuɗin wajen tallafa wa ɗalibai da dama a cikin Najeriya.

A cewarsa, hakan ya sa gwamnatin ta ga cewa ci gaba da yarjejeniyar ilimin ƙasashen biyu (Bilateral Education Agreement) a tsohon tsarin ba zai yi amfani ba.

“Saboda haka, yarjejeniyar ilimin ƙasashen biyu ba ta sake yi mana ma’ana a gwamnati ba. Hanya ce ta ɓarnatar da kuɗin gwamnati,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ba za ta yi almubazzaranci da kuɗin jama'a ba.

Ba a bar ɗaliban da ke karatu ba

Gwamnatin ta kuma bayyana cewa matakin ba yana nufin za ta yi watsi da ɗaliban da tuni suke karatu a ƙarƙashin tsohon tsarin tallafin ba.

An ce waɗannan ɗalibai za su ci gaba da samun tallafi har zuwa lokacin da suka kammala karatunsu, yayin da ba za a ƙara bayar da sabbin tallafin gwamnati a ƙarƙashin tsarin ba.

Haka kuma, matakin ba ya nufin an haramta wa ‘yan Najeriya samun tallafin karatu daga ƙasashen waje.

Ministan ya ce ƙasashen da suke son ci gaba da ɗaukar nauyin karatun ɗaliban Najeriya za su iya yin hakan, ba tare da sai gwamnatin Najeriya ta biya wani ɓangare na kuɗin ba.

“Amma idan ka dakatar da tallafin, sai ka ce ƙasashen da suke son ci gaba da bayar da tallafin karatu su ci gaba da yin hakan,” in ji Alausa.

Dalilin da ya sa aka sake duba tsarin

Ministan ya ce lokacin da aka fara irin waɗannan shirye-shiryen kimanin shekaru 20 da suka gabata, Najeriya ba ta da isasshen guraben karatu da ƙwarewar da ake buƙata a wasu fannoni.

Sai dai ya ce tun daga lokacin, Najeriya ta samu ci gaba sosai wajen gina jami'o'i, kwalejojin fasaha da kwalejojin ilimi.

“Lokacin da aka kafa waɗannan shirye-shiryen shekaru 20 da suka gabata, an yi su ne domin a tura ɗalibai makarantun gwamnati a ƙasashen waje saboda ba mu da isasshen ƙarfi a nan,” in ji shi.

“Amma a cikin shekaru 20 da suka gabata, mun gina ƙwarewa da dama a manyan makarantunmu — jami'o'i, kwalejojin fasaha da kwalejojin ilimi,” ya ƙara da cewa.

Gwamnatin Tarayya ta ce sake duba tsarin tallafin karatun na daga cikin sauye-sauyen da Ma'aikatar Ilimi ke aiwatarwa domin inganta tsarin ilimin Najeriya da kuma mayar da shi cikin abubuwan da suka fi muhimmanci a ƙarƙashin ajandar Renewed Hope ta gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

DA DUMI-DUMI

Gwamnati za ta fara karɓar kuɗin wutar lantarki daga jami’o’i da asibitoci – Ministan Wuta

Wasu jami’o’i sun zo wurina domin su gode min bayan sun shafe shekara biyu suna amfani da wutar lantarki kyauta. Na ce musu, mun gode, amma lokacin kyautar ya ƙare. Yanzu za mu zo mu ƙaddamar da tsarin, kuma za ku biya kuɗin wutar lantarki,” in ji shi.

Shin Muna Tunanin Za Mu Yi Watsi da Almajirai Mu Samu Zaman Lafiya?

Shin Arewa na tunanin za ta bar ’ya’yanta da mata suna yawo a kan tituna cikin talauci da rashin gata, sannan ta yi tsammanin samun zaman lafiya da ci gaba? 

Daga 1 ga Octoba WhatsApp zai fara cazar kuɗi kan saƙonnin da ake tura wa na kasuwanci

Sabon tsarin zai shafi kamfanoni da ke amfani da WhatsApp Business Platform, wadda aka fi sani da WhatsApp Business API, wajen tura saƙonni ga dimbin kwastomomi.

Dino Melaye ya shawarci Tinubu da iyalansa su fara tattara kayansu daga Villa – APC za ta sha kaye a 2027

Melaye ya ce matsalolin yunwa, kashe-kashe da sata sun nuna cewa akwai babban gibi tsakanin gwamnati da al’ummar ƙasar.

NELFUND: Mun raba wa ɗalibai miliyan 1.2 Naira biliyan 322 -Gwamnatin Tarayya 

Shugaba Tinubu ya ce ana buƙatar NELFUND ya kasance mai isasshen kuɗi kuma mai ɗorewa domin ci gaba da biyan buƙatun ɗaliban Najeriya.

Kanun Labarai

Hare-haren ’yan bindiga ya kashe mutane fiye da 10,000 cikin shekaru biyu na gwamnatin Tinubu – Amnesty

Amnesty ta ƙara da cewa ɗaruruwan ƙauyuka sun fuskanci hare-hare tare da tilasta wa mazauna barin gidajensu a jihohin Benue, Borno, Katsina, Sokoto, Plateau da Zamfara.

Gwamnatin Tinubu za ta dawo da binciken mai a Arewa bayan tsaida aikin tun bayan hawansa mulki 

Shugaban RMAFC ya kuma ce Shugaba Bola Ahmed Tinubu na damuwa da yadda aikin ya tsaya, yana mai cewa an ba gwamnonin Bauchi da Gombe tabbacin cewa za a sake tura kayan aiki da ma'aikata domin ci gaba da aikin.

Duk wanda ya ce bai amfana da tallafin Tinubu ba, to baya Najeriya – Gwamnan Sokoto, Ahmed Aliyu 

Gwamnan ya kuma yi kira ga ’yan Najeriya da su sake zaben Bola Tinubu a 2027, yana mai cewa yana da yakinin shugaban zai ci gaba da kawo sauyi a kasar.
spot_img

Labarai masu alaka

Sauran bangarori

spot_imgspot_img