UAE Za Ta Zuba Jarin Dala Biliyan $71 a Afirka, Domin Zurfafa Haɗin Gwiwa da Nahiyar

UAE Za Ta Zuba Jarin Dala Biliyan $71 a Afirka, Domin Zurfafa Haɗin Gwiwa da Nahiyar

Daga Wakiliya

WAKILIYA – Ƙasar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE) ta bayyana cewa za ta ƙara ƙarfafa haɗin gwiwarta da ƙasashen Afirka, inda ta fi mayar da hankali kan makamashi mai tsafta, gine-ginen more rayuwa da kuma fasahar zamani domin bunƙasa tattalin arzikin nahiyar.

Ministan Ƙasa na UAE, Saeed bin Mubarak Al Hajeri, ya ce ƙasarsa na kallon Afirka a matsayin muhimmiyar abokiyar hulɗa a shirinta na faɗaɗa tattalin arziƙi da rage dogaro da man fetur.

Al Hajeri ya bayyana cewa tsakanin shekarun 2021 zuwa 2025, UAE ta zuba kusan dala biliyan 71.32 a ƙasashen yankin Hamada (Sub-Saharan Africa).

Ya ƙara da cewa UAE ta ware sama da dala biliyan 70 domin ayyukan makamashi mai tsafta da kore a faɗin nahiyar, ta hannun shirye-shirye irin su Masdar da kuma dandalin Etihad 7.

A cewarsa, ƙasar na kuma ƙara zuba jari a fannin hanyoyi, tashoshin jiragen ruwa da dabarun sufuri ta hanyar kamfanonin DP World, AD Ports Group, da kuma tallafin Abu Dhabi Fund for Development.

Ministan ya ce waɗannan jarin za su taimaka wajen rage tsadar kasuwanci, inganta hanyoyin sufuri, faɗaɗa samar da wutar lantarki, samar da ayyukan yi da kuma inganta musayar fasaha da ƙwarewa tsakanin UAE da ƙasashen Afirka.

Ya kuma bayyana cewa UAE ta rattaba hannu kan yarjejeniyoyin haɗin gwiwar tattalin arziƙi guda tara da ƙasashen Afirka, tare da burin kai cinikayyar ƙetare ta ƙasar zuwa dirham tiriliyan huɗu (AED4tn) nan da shekarar 2031.

Bugu da ƙari, Al Hajeri ya ce UAE ta ƙaddamar da wani shiri na dala biliyan ɗaya domin bunƙasa fasahar Basirar Wucin Gadi (AI) a Afirka, wanda aka sanar da shi a taron G20 da aka gudanar a Afirka ta Kudu.

Ya jaddada cewa UAE za ta ci gaba da aiki tare da gwamnatocin Afirka da kamfanoni masu zaman kansu wajen aiwatar da ayyukan da za su haɓaka ci gaba mai ɗorewa da samar da damarmakin tattalin arziƙi ga nahiyar.

DA DUMI-DUMI

2027: Matasan APC na Arewa Sun Yi Barazanar Janye Goyon Baya Ga Tinubu, Saboda Zargi Ana Nuna Musu Wariya

A cewar ƙungiyar, ta umarci shugabannin ƙungiyoyin goyon bayan APC 1,378 da ke jihohin Arewa 19 da Babban Birnin Tarayya Abuja su fara tattaunawa kan yiwuwar janye goyon baya ga takarar Tinubu ta wa'adi na biyu idan ba a saurari korafinsu ba.

Matsalar Rashin Amincewa Da Ke Hana Kasuwancin Intanet Bunƙasa a Najeriya Musamman Arewa

A yau, aika kuɗi ta banki ko manhajojin kuɗi ya zama abu mai sauƙi a Najeriya. Amma sauƙin tura kuɗi ba yana nufin an magance matsalar kasuwanci ba.

Kasar Guinea Ta Fice Daga Shirin Samar da Kuɗin Bai Ɗaya na ECOWAS -Ta Zabi Riƙe Kuɗinta

Ana sa ran shugabannin ECOWAS za su sake ganawa a watan Disamba domin tattauna sauran batutuwan da suka rage kafin fara amfani da kuɗin Eco.

Gaggawar Yaɗa Labaran da Ba a Tantance Ba Ka Iya Shafar Kasuwar Makamashi da Zuba Jari, Ya Jawo Tashin Farashi – NUPRC Ta Gargadi...

A ƙarshe, ta buƙaci 'yan jaridar da ke ba da rahotannin makamashi su mayar da hankali kan tantance bayanai, fahimtar alkaluma da kuma bayar da cikakken mahallin labari domin tabbatar da sahihanci da ƙarfafa amincewar jama'a.

Najeriya Ba Ta da Tattalin Kula da Abubuwan Da Aka Gina, Shi Yasa Kasar Ta Kasa Ci Gaba – Okonjo-Iweala

Mu a Najeriya ba mu da kyakkyawar al'adar kula da abubuwan da muka gina. Ni ma 'yar Najeriya ce, amma dole ne mu faɗi gaskiya," in ji ta.

Kanun Labarai

Malamin da ya shiga siyasa, aka yi ƙwaramniyar siyasa da shi, ya fi malamin da ya zauna kan buzun yana yi wa ‘yan siyasa...

Malamin da ya shiga siyasa, aka yi ƙwaramniyar siyasa da shi, ya fi malamin da ya zauna kan buzun yana yi wa 'yan siyasa addu'a -Dr. Ahmed Gumi

An Kashe Biliyoyin Naira Amma Duk da Haka Cibiyoyin Lafiya 6,516 Sun Gagara Aiki a Najeriya; Arewa Ce Kan Gaba

Jihar Katsina ce ke da mafi yawan cibiyoyin da ba sa aiki da guda 442, sai Osun da 406, yayin da Benue ke da 343, Enugu 335, Adamawa 286, sannan Borno na cikin jerin jihohin da ke fuskantar matsala.
spot_img

Labarai masu alaka

Sauran bangarori

spot_imgspot_img