Zaɓen 2027: Sarakuna a Kwara Sun Bayyana Goyon Bayansu Ga APC, Za Su Taya Jam’iyyar Yaƙin Neman Zaɓe

Daga Wakiliya

Majalisar Sarakunan Gargajiyar Kudancin Jihar Kwara ta bayyana cikakken goyon bayanta ga jam’iyyar APC, tare da alƙawarin wayar da kan al’umma domin tabbatar da nasarar jam’iyyar a zaɓen shekarar 2027.

Sarakunan sun ce sun ɗauki wannan matsaya ne saboda abin da suka bayyana a matsayin kyakkyawan aiki da ci gaban da Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq ya kawo a jihar, musamman a yankin Kudancin Kwara.

Da yake jawabi a madadin sarakunan yankunan Igbomina, Ibolo da Ekiti, Olupo na Ajase-Ipo, Oba Ismail Yahya Alebiosu, ya ce Majalisar Sarakunan Kudancin Kwara ta amince da goyon bayan ɗan takarar gwamna na APC daga Kwara ta Arewa, Yakubu Salihu, saboda tabbatar da adalci da daidaito.

Oba Alebiosu ya yabawa Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Gwamna AbdulRazaq bisa amincewa da buƙatar da aka gabatar na bai wa Kwara ta Arewa damar fitar da gwamna na gaba, yayin da yankin Igbomina zai fitar da ɗan takarar Sanatan Kudancin Kwara.

Sarkin ya kuma yi alƙawarin cewa dukkan sarakunan gargajiya na Kudancin Kwara za su ba APC cikakken goyon baya tare da yin duk abin da doka ta amince da shi domin jam’iyyar ta yi nasara a zaɓen 2027.

Hakazalika, Elerin na Erin-Ile, Oba Jimoh Adebowale Adesoye, ta bakin Onipe na Ipee, Oba Muftau Adebayo Lawal Titiloye III, ya ce al’ummar yankin Oyun za su mara wa APC baya saboda irin ayyukan ci gaban da gwamnatin AbdulRazaq ta gudanar.

Shi ma Olofa na Offa, Oba Mufutau Gbadamosi Esuwye, ya bayyana kwarin gwiwarsa cewa ‘yan takarar APC a jihar Kwara za su samu nasara a zaɓen 2027.

A nasa jawabin, Shugaban APC na Jihar Kwara, Prince Sunday Fagbemi, ya gode wa sarakunan gargajiya da al’ummar yankunan Oyun, Offa da Irepodun bisa goyon bayan da suka nuna ga jam’iyyar da kuma yadda aka gudanar da zaɓen fidda gwani cikin lumana.

DA DUMI-DUMI

Ku Rika Zuwa Filin Jirgin Sama Aƙalla Sa’o’i Uku Kafin Tashin Jirginku – NCAA Ta Gargadi Matafiya

Ya kuma buƙaci fasinjoji da su yi amfani da tsarin rajista ta intanet (online check-in) idan hakan ya yiwu, tare da zaɓen kujerarsu tun kafin isa filin jirgin.

2027: Matasan APC na Arewa Sun Yi Barazanar Janye Goyon Baya Ga Tinubu, Saboda Zargi Ana Nuna Musu Wariya

A cewar ƙungiyar, ta umarci shugabannin ƙungiyoyin goyon bayan APC 1,378 da ke jihohin Arewa 19 da Babban Birnin Tarayya Abuja su fara tattaunawa kan yiwuwar janye goyon baya ga takarar Tinubu ta wa'adi na biyu idan ba a saurari korafinsu ba.

UAE Za Ta Zuba Jarin Dala Biliyan $71 a Afirka, Domin Zurfafa Haɗin Gwiwa da Nahiyar

Ya jaddada cewa UAE za ta ci gaba da aiki tare da gwamnatocin Afirka da kamfanoni masu zaman kansu wajen aiwatar da ayyukan da za su haɓaka ci gaba mai ɗorewa da samar da damarmakin tattalin arziƙi ga nahiyar.

Matsalar Rashin Amincewa Da Ke Hana Kasuwancin Intanet Bunƙasa a Najeriya Musamman Arewa

A yau, aika kuɗi ta banki ko manhajojin kuɗi ya zama abu mai sauƙi a Najeriya. Amma sauƙin tura kuɗi ba yana nufin an magance matsalar kasuwanci ba.

Kasar Guinea Ta Fice Daga Shirin Samar da Kuɗin Bai Ɗaya na ECOWAS -Ta Zabi Riƙe Kuɗinta

Ana sa ran shugabannin ECOWAS za su sake ganawa a watan Disamba domin tattauna sauran batutuwan da suka rage kafin fara amfani da kuɗin Eco.

Kanun Labarai

Gaggawar Yaɗa Labaran da Ba a Tantance Ba Ka Iya Shafar Kasuwar Makamashi da Zuba Jari, Ya Jawo Tashin Farashi – NUPRC Ta Gargadi...

A ƙarshe, ta buƙaci 'yan jaridar da ke ba da rahotannin makamashi su mayar da hankali kan tantance bayanai, fahimtar alkaluma da kuma bayar da cikakken mahallin labari domin tabbatar da sahihanci da ƙarfafa amincewar jama'a.

Najeriya Ba Ta da Tattalin Kula da Abubuwan Da Aka Gina, Shi Yasa Kasar Ta Kasa Ci Gaba – Okonjo-Iweala

Mu a Najeriya ba mu da kyakkyawar al'adar kula da abubuwan da muka gina. Ni ma 'yar Najeriya ce, amma dole ne mu faɗi gaskiya," in ji ta.
spot_img

Labarai masu alaka

Sauran bangarori

spot_imgspot_img