Daga Wakiliya
Wasu ƙungiyoyin matasan jam’iyyar APC daga Arewacin Najeriya sun yi barazanar janye goyon bayansu ga takarar Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaɓen 2027 idan ba a magance abin da suka kira nuna musu wariya da rashin ba su damar shiga harkokin siyasa ba.
Barazanar ta biyo bayan wata ganawa da ta haɗa North-West APC Youth Stakeholders Forum, ƙarƙashin jagorancin Bashir Ruma, da Arewa Democratic Youth Stakeholders Forum.
A cikin wata sanarwa da Sakataren Yaɗa Labarai na ƙungiyar, Salawudeen Shaibu Planner, ya sanya wa hannu, ƙungiyar ta ce an ware matasan Arewa daga muƙaman siyasa, shugabancin matasa da kuma yanke muhimman shawarwari a cikin jam’iyyar APC da gwamnatin tarayya.
Ƙungiyar ta ce za ta fara tattara ƙungiyoyin magoya bayan APC a faɗin Arewa domin adawa da abin da ta bayyana a matsayin rashin adalci da siyasar nuna bambancin yanki.
Har ila yau, ta naɗa Haruna Sardauna a matsayin mai kula da yankin Arewa maso Gabas, yayin da aka naɗa Idiriss Jibrin domin jagorantar yankin Arewa ta Tsakiya.
Ƙungiyar ta kuma yi zargin cewa ɗan Shugaba Tinubu, Seyi Tinubu, na da tasiri wajen naɗe-naɗen matasa da shugabanci, inda ta ce ana fifita mutanen Kudu maso Yamma, musamman Yarabawa, lamarin da ta ce ya sa matasan Arewa ke jin an mayar da su saniyar ware.
Ta ambaci Ma’aikatar Raya Matasa, shugabancin matasan APC, NANS, NYCN da sauran ƙungiyoyin matasa a matsayin wuraren da ta ce ana samun rashin daidaito.
Haka kuma, ƙungiyar ta yi zargin cewa ƙungiyoyin City Boy Movement da Relax, Tinubu Is Fixing Nigeria Movement sun samu fifiko saboda alaƙarsu da Seyi Tinubu, yayin da ake matsa wa ƙungiyoyin Arewa su yi aiki tare da su.
A cewar ƙungiyar, ta umarci shugabannin ƙungiyoyin goyon bayan APC 1,378 da ke jihohin Arewa 19 da Babban Birnin Tarayya Abuja su fara tattaunawa kan yiwuwar janye goyon baya ga takarar Tinubu ta wa’adi na biyu idan ba a saurari korafinsu ba.
Ƙungiyar ta jaddada cewa kuri’un Arewa sun taka muhimmiyar rawa wajen nasarar Tinubu a zaɓen 2023, don haka ta ce ya dace a bai wa yankin damar da ta dace a muƙamai da damar siyasa.
Duk da haka, Bashir Ruma ya buƙaci matasan Arewa su ci gaba da kasancewa masu zaman lafiya yayin da suke neman adalci da wakilci.
Ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, Fadar Shugaban Ƙasa, shugabancin APC na ƙasa da kuma Seyi Tinubu ba su fitar da wata sanarwa kan waɗannan zarge-zarge ba.



