Daga Wakiliya
Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani, ya bayyana cewa yana da cikakken yaƙinin Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai samu aƙalla kashi 95 cikin 100 na ƙuri’un Kaduna a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
Uba Sani ya bayyana hakan ne a ranar Talata yayin ƙaddamar da aikin gina titin Kaduna–Birnin Gwari mai tsawon kilomita 122, inda ya ce a ganinsa sakamakon zaɓen 2027 a Kaduna ya riga ya tabbata.
Ya ce Kaduna ita ce cibiyar siyasa da tattalin arziƙin Arewacin Najeriya, yana mai yabawa Shugaba Tinubu kan irin ayyukan ci gaba da gwamnatin sa ke aiwatarwa a yankin.
Gwamnan ya kuma ce babu wani shugaban Najeriya da ya taɓa aiwatar da ayyukan raya Arewacin ƙasar kamar yadda Tinubu yake yi a yanzu.
A cewarsa, ya taɓa bayyana hakan watanni biyu da suka gabata kuma har yanzu babu wanda ya kawo hujjar da ta karyata ikirarinsa.
Uba Sani ya ƙara da cewa ayyukan da ake gudanarwa a sassan Arewacin Najeriya sun nuna irin kulawar da Shugaba Tinubu ke bai wa yankin, yana mai gode masa saboda abin da ya kira ƙaunar Arewa da ci gaban ƙasa.





