Daga Wakiliya
Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Najeriya (NCAA) ta shawarci fasinjojin da ke tafiya zuwa ƙasashen waje da su rika isa filin jirgin sama aƙalla sa’o’i uku kafin lokacin tashin jirginsu domin kauce wa rasa jirgi sakamakon jinkiri.
Daraktan Hulɗa da Jama’a na hukumar, Michael Achimugu, ne ya bayar da wannan shawara a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X ranar Litinin.
Achimugu ya bayyana cewa lokutan rufe wuraren rajistar shiga jirgi (check-in) sun bambanta daga kamfanin jirgin sama zuwa wani, don haka ya kamata matafiya su yi gaggawar isa filin jirgi.
Ya kuma buƙaci fasinjoji da su yi amfani da tsarin rajista ta intanet (online check-in) idan hakan ya yiwu, tare da zaɓen kujerarsu tun kafin isa filin jirgin.
A cewarsa, “Ya fi kyau mutum ya isa filin jirgin da wuri fiye da ya makara har ya rasa jirginsa.”
Wannan shawara na zuwa ne yayin da NCAA ke ƙoƙarin rage yawan fasinjojin da ke rasa jirage ko fuskantar tsaiko sakamakon isa filin jirgin a makare.




