Daga Wakiliya
Ƙungiyar Kabilar Mutanen Igbo, (Igbo Community Association, ICA), ta yi watsi da kalaman Gwamnan Jihar Imo, Hope Uzodimma, Ministan Ayyuka, David Umahi, da Mataimakin Babban Mai Tsawatarwa na Majalisar Dattawa, Onyekachi Nwebonyi, inda suka ce ba su da hurumin yin magana da yawun al’ummar Igbo kan zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
Shugaban ƙungiyar, Nze Engr. Ikenna Ellis-Ezenekwe, ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa mutanen uku ba su wakiltar ra’ayin al’ummar Igbo, yana mai zargin cewa suna kare muradun siyasar kansu ne ta hanyar nuna goyon baya ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Ellis-Ezenekwe ya ce masu riƙe da muƙaman siyasa ba su da ikon ayyana matsayar siyasa a madadin miliyoyin ‘yan kabilar Igbo, yana mai cewa goyon bayan da suka nuna ra’ayin kansu ne, ba na al’umma baki ɗaya ba.
Ya ƙara da cewa al’ummar Kudu maso Gabas na ganin gwamnatin Tinubu ta gaza wajen magance matsalolin tattalin arziki da gudanar da mulki, saboda haka ikirarin cewa shugaban zai lashe jihohin yankin biyar a zaɓen 2027 ba gaskiya bane.
Ƙungiyar ta kuma buƙaci jami’an gwamnati daga Kudu maso Gabas su mayar da hankali kan ayyukan da kundin tsarin mulki ya ɗora musu da kuma magance matsalolin tattalin arzikin al’umma, maimakon yin magana a madadin dukkan ‘yan Igbo kan batutuwan siyasa.





