Kalaman Jingir na da matuƙar tayar da hankali— Fani-Kayode ya caccaki malamin kan salon tallata tikitin Musulmi-Musulmi

Kalaman Jingir na da matuƙar tayar da hankali” — Fani-Kayode ya caccaki malamin kan tallata tikitin Musulmi-Musulmi

Daga Wakiliya

Jakadan Najeriya mai jiran gado a Afirka ta Kudu, Femi Fani-Kayode, ya soki kalaman wani malamin addinin Musulunci, Sheikh Yahya Jingir, na kira ga ci gaba da tikitin Musulmi da Musulmi a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

Sheikh Yahya Jingir ya bayyana cewa shi ne jagoran goyon bayan tikitin Musulmi da Musulmi, yana mai kira ga Musulmi su haɗa kai wajen tabbatar da nasarar irin wannan tikiti a zaɓen 2027.

A wani bidiyo da ya yaɗu a kafafen sada zumunta, Sheikh Jingir ya kuma yi kira ga Musulmi su mallaki katunan zaɓensu domin tunkarar zaɓen.

Ya ce bai ga laifi ba wajen yin kira ga tikitin Musulmi da Musulmi, duk da cewa ya san cewa wasu Kiristoci da mabiya sauran addinai ba sa goyon bayan hakan.

Sai dai Femi Fani-Kayode ya ce kalaman malamin na da matuƙar tayar da hankali, kuma irin wannan magana ba ta taimaka wajen haɗin kan Najeriya.

Fani-Kayode ya ce Najeriya ba ƙasar Musulmi ba ce, kuma ba ƙasar Kirista ba ce, illa dai ƙasa ce mai bin tsarin zaman duniya tare da ƙabilu da addinai daban-daban.

Ya bayyana cewa goyon bayansa ga tikitin Musulmi da Musulmi a 2027, kamar yadda ya yi a 2023, ya samo asali ne daga cancanta, ƙwarewa, halayya da kuma ƙarfin ’yan takarar wajen lashe zaɓe, ba wai saboda addininsu ba.

Ya ce idan lokaci ya yi, Najeriya ma za ta iya samun tikitin Kirista da Kirista, yana mai kira ga ’yan ƙasar da su mayar da hankali kan manufofi, ƙwarewa da halayen ’yan takara maimakon addini.

Fani-Kayode ya kuma yi gargadin cewa bai kamata batun tikitin addini ya raba kan ’yan Najeriya ba, yana mai cewa “mu ’yan Najeriya ne kafin mu zama Musulmi ko Kirista.”

Kalaman Sheikh Jingir sun jawo ce-ce-ku-ce a kafafen sada zumunta, inda wasu ke ganin sun yi tsauri, yayin da wasu ke kare damar kowane ɗan Najeriya na zaɓar irin ɗan takarar da yake so ba tare da la’akari da addini ba.

DA DUMI-DUMI

Tinubu ya nemi haɗin kan Tijjaniyya wajen yaƙi da tsattsauran ra’ayi a Najeriya da yankin Sahel

Tinubu ya ce ya kamata malaman addini su riƙa jan hankalin shugabannin siyasa kan adalci, ɗaukar nauyi da tausayi, tare da jan hankalin jama’a da kada su mayar da ƙorafe-ƙorafe zuwa hujjar aikata rashin doka.

Har yanzu Atiku, da Obi da Kwankwaso na da damar hada kai domin kawar da Tinubu a 2027 -Ologbondiyan

Ya ce burin ADC shi ne samar da gwamnati da za ta yi aiki domin amfanin ’yan Najeriya tare da tabbatar da cewa dimokuradiyya ta amfani al’umma.

Duk wanda ya ce ’yan Najeriya na shan wahala ƙarƙashin Tinubu, ƙarya yake -Abu Ammar Shugaban Hisbah na Katsina

Duk wanda ya ce ’yan Najeriya na shan wahala ƙarƙashin Tinubu, ƙarya yake -mutanen da a baya ba sa iya sayen abinci yanzu suna iya saya -Abu Ammar Shugaban Hisbah na Katsina

Kamfanin Amurka ya ƙera rigar da ba ta bukatar wanki ko da mutum zai rika saka ta na tsawon wata guda

HercLeon, wanda a baya ya ƙera kayan sawa da ya ce suna taimakawa wajen rage wari, ya bayyana HercShirt V5.0 a matsayin rigar da za ta iya daɗewa fiye da rigunan da ake wankewa akai-akai.

Tinubu ya sauya tsarin tattalin arzikin Najeriya — Shugaban NRS Zacch Adedeji

Ya kawo misalin Andy Burnham na Birtaniya, inda ya ce ya ɗauki matakai da suka haɗa da rage haraji kan wutar lantarki ta gidaje da kuma rage kuɗin sufuri domin sauƙaƙa wa jama’a.

Kanun Labarai

Akalla makarantun firamare da sakandare 65 sun daina aiki ko aka rufe a Arewacin Najeriya saboda rashin tsaro -rahoto

makarantun suna jihohin Sokoto, Benue, Plateau, Borno, Kaduna da Kebbi, yayin da rashin tsaro ya kuma kawo cikas ga karatun yara a wasu sassan Katsina da Adamawa.

Mun shafe fiye da shekara uku muna soyayya, amma tsadar rayuwa ta hana mu aure  – inji ma’auratan da aka yi wa Auren Gata...

Ta ce tana matukar son mijinta, kuma tana fatan za su rayu cikin zaman lafiya da fahimtar juna, tare da gina aure da wasu za su yi koyi da shi.

Rayuwa a Sambisa: Tsoffin mayakan Boko Haram sun bayyana yadda aka yaudare su

Rayuwa a Sambisa: Tsoffin mayakan Boko Haram sun bayyana yadda aka yaudare su - Dole ne al'umma ta yi hakuri ta karbe su, domin idan ba haka ba, akwai yiwuwar wasu su koma daji. - Hukumomi
spot_img

Labarai masu alaka

Sauran bangarori

spot_imgspot_img