Daga Wakiliya
Babu gaskiya a labarin cewa Sarki Sanusi ya samu ‘carry over’ — Masarautar Kano
Masarautar Kano ta musanta wani faifan bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta, wanda ke ikirarin cewa Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya fadi wani darasi a karatunsa na Shari’a a Jami’ar Northwest da ke Kano.
Sakataren ofishin Sarkin, Muhammad Ado, ya ce labarin ba gaskiya ba ne, yana mai cewa maki guda ne kawai ya rage wa Sarkin domin samun digiri mai daraja ta farko.
Wani dalibi a jami’ar ya tabbatar da cewa har yanzu ba a fara jarabawar ba, kuma ana sa ran fara ta ne ranar Litinin.
Masarautar ta kuma ce bidiyon da ake yaɗawa an dauke shi ne yayin wani shiri da ɗaliban Shari’a suka gudanar, inda wasu matasa suka shirya shi da nufin yaɗa bayanan ƙarya.




