Tinubu ya nemi haɗin kan Tijjaniyya wajen yaƙi da tsattsauran ra’ayi a Najeriya da yankin Sahel

Tinubu ya nemi haɗin kan Tijjaniyya wajen yaƙi da tsattsauran ra’ayi a Najeriya da yankin Sahel

Daga Wakiliya

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya nemi ƙungiyoyin Tijjaniyya da sauran ƙungiyoyin addini a Afirka su ƙara haɗa kai da gwamnatoci wajen yaƙi da ta’addanci da sauran matsalolin tsaro da ke addabar yankin Sahel da Yammacin Afirka.

Tinubu ya yi wannan kiran ne a Kano ranar Lahadi, a wani saƙon fatan alheri da Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume, ya isar a madadinsa a wajen babban Mauludin Sheikh Ahmad Al-Tijani, RTA.

Shugaban ya ce ƙungiyoyin addini da ke da faɗaɗɗun hanyoyin sadarwa a ƙasashe daban-daban na da babbar damar taimakawa wajen yaƙi da ta’addanci, garkuwa da mutane, ’yan bindiga da sauran nau’o’in tsattsauran ra’ayi.

Ya bukaci malaman addini da shugabannin waliyyai da su yi amfani da tasirinsu wajen wayar da kan jama’a kan zaman lafiya, koyar da matasa, sasanta rikice-rikice da kuma hana amfani da addini wajen haddasa tashin hankali.

Bola Ahmed Tinubu ya ce yaɗuwar ƙungiyar Tijjaniyya a Yammacin Afirka, Arewacin Afirka da sauran sassan duniya ya sanya ta cikin kyakkyawan matsayi na taka rawa wajen samar da zaman lafiya a yankin Sahel.

“Dole kuyi amfani da muryoyinku wajen yin Allah-wadai da kisan mutane marasa laifi, ta’addanci, garkuwa da mutane, ’yan bindiga da kuma amfani da addini wajen halatta zalunci,” in ji shugaban.

Ya kuma ce shugabannin addini na da rawar da za su taka wajen ilmantar da jama’a kan zaman lafiya, fahimtar addini da kuma tarbiyyar matasa.

Tinubu ya ce ya kamata malaman addini su riƙa jan hankalin shugabannin siyasa kan adalci, ɗaukar nauyi da tausayi, tare da jan hankalin jama’a da kada su mayar da ƙorafe-ƙorafe zuwa hujjar aikata rashin bin doka.

Ya ce gwamnatin tarayya na son ƙara haɗa gwiwa da shugabannin addini da na gargajiya wajen samar da zaman lafiya daga matakin al’umma, yaƙi da yaɗa labaran ƙarya da ƙarfafa haɗin kan ƙasa.

Shugaban ya kuma jaddada cewa matsayin Najeriya a matsayin ƙasa da ta haɗa Yammacin Afirka, yankin Sahel, tafkin Chadi da Tekun Guinea ya sa zaman lafiyarta ke da tasiri ga sauran ƙasashen yankin.

A cewarsa, ƙungiyoyin Tijjaniyya da ke da alaƙa a ƙasashe da dama za su iya taimakawa wajen gina tsarin zaman lafiya da zai ƙara ƙarfi ga ƙoƙarin gwamnati da hukumomin yankin.

Taron Mauludin ya samu halartar Khalifan Tijjaniyya na duniya, malamai, shugabannin addini da mabiya daga Najeriya da wasu ƙasashe, ciki har da Aljeriya, Maroko, Senegal da Masar.

Tinubu ya kuma karrama marigayi Sheikh Dahiru Usman Bauchi, wanda ya rasu a watan Nuwamban 2025, yana mai bayyana shi a matsayin malami, uba kuma mai kishin zaman lafiya da matsakaicin ra’ayi.

Ya ce hanya mafi kyau ta girmama Sheikh Dahiru Bauchi ita ce ci gaba da ayyukan da ya gada na koyar da Alƙur’ani, tarbiyya, neman ilimi da zaman lafiya tsakanin al’umma.

DA DUMI-DUMI

Kalaman Jingir na da matuƙar tayar da hankali— Fani-Kayode ya caccaki malamin kan salon tallata tikitin Musulmi-Musulmi

A wani bidiyo da ya yaɗu a kafafen sada zumunta, Sheikh Jingir ya kuma yi kira ga Musulmi su mallaki katunan zaɓensu domin tunkarar zaɓen.

Har yanzu Atiku, da Obi da Kwankwaso na da damar hada kai domin kawar da Tinubu a 2027 -Ologbondiyan

Ya ce burin ADC shi ne samar da gwamnati da za ta yi aiki domin amfanin ’yan Najeriya tare da tabbatar da cewa dimokuradiyya ta amfani al’umma.

Duk wanda ya ce ’yan Najeriya na shan wahala ƙarƙashin Tinubu, ƙarya yake -Abu Ammar Shugaban Hisbah na Katsina

Duk wanda ya ce ’yan Najeriya na shan wahala ƙarƙashin Tinubu, ƙarya yake -mutanen da a baya ba sa iya sayen abinci yanzu suna iya saya -Abu Ammar Shugaban Hisbah na Katsina

Kamfanin Amurka ya ƙera rigar da ba ta bukatar wanki ko da mutum zai rika saka ta na tsawon wata guda

HercLeon, wanda a baya ya ƙera kayan sawa da ya ce suna taimakawa wajen rage wari, ya bayyana HercShirt V5.0 a matsayin rigar da za ta iya daɗewa fiye da rigunan da ake wankewa akai-akai.

Tinubu ya sauya tsarin tattalin arzikin Najeriya — Shugaban NRS Zacch Adedeji

Ya kawo misalin Andy Burnham na Birtaniya, inda ya ce ya ɗauki matakai da suka haɗa da rage haraji kan wutar lantarki ta gidaje da kuma rage kuɗin sufuri domin sauƙaƙa wa jama’a.

Kanun Labarai

Akalla makarantun firamare da sakandare 65 sun daina aiki ko aka rufe a Arewacin Najeriya saboda rashin tsaro -rahoto

makarantun suna jihohin Sokoto, Benue, Plateau, Borno, Kaduna da Kebbi, yayin da rashin tsaro ya kuma kawo cikas ga karatun yara a wasu sassan Katsina da Adamawa.

Mun shafe fiye da shekara uku muna soyayya, amma tsadar rayuwa ta hana mu aure  – inji ma’auratan da aka yi wa Auren Gata...

Ta ce tana matukar son mijinta, kuma tana fatan za su rayu cikin zaman lafiya da fahimtar juna, tare da gina aure da wasu za su yi koyi da shi.

Rayuwa a Sambisa: Tsoffin mayakan Boko Haram sun bayyana yadda aka yaudare su

Rayuwa a Sambisa: Tsoffin mayakan Boko Haram sun bayyana yadda aka yaudare su - Dole ne al'umma ta yi hakuri ta karbe su, domin idan ba haka ba, akwai yiwuwar wasu su koma daji. - Hukumomi
spot_img

Labarai masu alaka

Sauran bangarori

spot_imgspot_img