Har yanzu Atiku, da Obi da Kwankwaso na da damar hada kai domin kawar da Tinubu a 2027 -Ologbondiyan
Daga Wakiliya
Tsohon Sakataren Yada Labarai na Jam’iyyar PDP na Kasa, Kola Ologbondiyan, ya ce har yanzu akwai damar manyan ’yan adawa irin su Atiku Abubakar, Peter Obi da Rabiu Kwankwaso su sake hada kai domin kalubalantar Shugaba Bola Tinubu a zaben 2027.
Mista Ologbondiyan, wanda yanzu yake mai ba Shugaban Jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), Sanata David Mark, shawara kan harkokin yada labarai, ya ce taron da jam’iyyun adawa suka gudanar a Ibadan ya samar da tsarin da zai iya kai ga hada kansu a zabe mai zuwa.
Ya ce ko da Peter Obi da Rabiu Kwankwaso sun fice daga kawancen a watan Mayun 2026, har yanzu ba a rufe kofar sake samun babban kawance tsakanin jam’iyyun adawar ba.
“Babu wani matsaya da aka cimma da ta wajabta musu ficewa daga kawancen, domin tattaunawa tana ci gaba,” in ji shi.
Kola Ologbondiyan ya kuma ce abin da ya fi dacewa shi ne jam’iyyun adawar su hada kai, su tsayar da dan takara guda, domin samun damar kalubalantar jam’iyyar APC a zaben 2027.
‘Ba adawa ce za ta hana Tinubu barci ba’
Da yake magana kan kalaman Shugaba Bola Tinubu na cewa zai yi “fada har karshe” a siyasar 2027, Ologbondiyan ya ce shugaban bai kamata ya dauki zaben a matsayin fafatawa tsakaninsa da jam’iyyun adawa kadai ba.
A cewarsa, babban kalubalen shugaban zai fito ne daga ’yan Najeriya da ke fama da matsin tattalin arziki, yunwa da karancin kudi.
Ya ce miliyoyin ’yan Najeriya za su yi amfani da kuri’unsu wajen bayyana ra’ayinsu kan yadda suke kallon yadda gwamnati ta tafiyar da kasar.
“Batun ba tsakanin shugaban kasa da jam’iyyun adawa ba ne. Batun yana tsakanin shugaban kasa da ’yan Najeriya da ke fama da yunwa, wadanda ba su da kudi a aljihunsu,” in ji Ologbondiyan.
Ya kuma ce babu bukatar jam’iyyun adawa su rika gaya wa ’yan Najeriya cewa rayuwa ta yi sauki, domin su kansu ’yan kasar sun san halin da suke ciki.
‘PDP na cikin wani yanayi’
Dangane da makomar PDP, Ologbondiyan ya ce babban abin da ke damunsa shi ne rashin tabbas kan jam’iyyar da ake magana a kai.
Ya ce yayin da PDP ta rasa mulki a shekarar 2015, an yi tsammanin za ta zama babbar jam’iyyar adawa, amma a ganinsa, PDP din da ake da ita yanzu ba ta cika wannan matsayi ba.
Ologbondiyan ya kuma kare ADC, yana mai cewa jam’iyyar ta mayar da hankali wajen kare dimokuradiyya da adawa da tsarin da ke bai wa mutum daya iko fiye da kima.
Ya ce burin ADC shi ne samar da gwamnati da za ta yi aiki domin amfanin ’yan Najeriya tare da tabbatar da cewa dimokuradiyya ta amfani al’umma.
A cewarsa, babban abin da ya kamata ya hada ’yan adawa a yanzu shi ne yadda za a yi amfani da hanyoyin dimokuradiyya wajen kawo sauyi da dakatar da abin da ya kira ci gaba da wahalar ’yan Najeriya.




