2027: “Mutanen da ba za su iya faɗin makarantar firamare da suka yi ba suna neman zama shugaban ƙasa” – Rufai Oseni
Fitaccen ɗan jarida kuma mai gabatar da shirin safe na Arise Television, Rufai Oseni, ya soki wasu daga cikin bayanan da aka wallafa game da ‘yan takarar shugaban ƙasa na zaɓen 2027, yana mai cewa ya kamata ‘yan Najeriya su tambayi duk wanda ke neman shugabancin ƙasa amma bai bayyana tarihin makarantar firamare da ya yi ba.
A wani saƙo da ya wallafa a Facebook, Rufai Oseni ya ce:
“Mutanen da ba za su iya gaya muku makarantar firamare da suka yi ba suna neman zama shugaban ƙasa, kuma ‘yan Najeriya za su zaɓe su.”
Kalaman nasa sun biyo bayan wallafa bayanan sirri da takardun neman takarar shugaban ƙasa da Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta (INEC) ta yi domin bai wa jama’a damar duba su.
Takardun sun nuna cewa ɗan takarar APC, Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana digirinsa na farko daga Chicago State University ne kawai, yayin da aka rubuta “0000” a wuraren da ake tambayar shekarun da ya yi makarantar firamare da sakandare.
Sai dai takardun da Peter Obi na jam’iyyar NDC da kuma Atiku Abubakar na ADC suka gabatar sun ƙunshi tarihin karatunsu tun daga makarantar firamare.
A nasa martanin, tsohon Sanatan Kogi ta Yamma, Dino Melaye, ya ce Tinubu bai gabatar da bayanan makarantar firamare da sakandare ba, yana tambayar yadda aka ba shi gurbin karatu a jami’a a ƙasashen waje idan ba tare da irin waɗannan bayanai ba.
INEC ta ce wallafa takardun ya ba jama’a damar duba su, kuma duk wanda ya gano bayanan ƙarya na da damar ƙalubalantar su a kotu kamar yadda Dokar Zaɓe ta tanada.





