Najeriya Ta Shiga Ƙawancen Tsaron Tekun Maliya (Red Sea) da Saudiyya Ke Jagoranta

Najeriya Ta Shiga Ƙawancen Tsaron Tekun Maliya (Red Sea) da Saudiyya Ke Jagoranta

Daga Wakiliya

Najeriya ta shiga cikin ƙasashe 14 da suka amince da kafa wata haɗaɗɗiyar ƙungiyar tsaron teku ƙarƙashin jagorancin Saudiyya domin kare jiragen kasuwanci da hanyoyin jigilar makamashi a yankin Tekun Maliya (Red Sea) da Tekun Gulf of Aden.

An cimma wannan matsaya ne bayan wani taro da aka gudanar a birnin Riyadh, inda wakilan ƙasashe 43 da kuma Tarayyar Turai suka tattauna kan yadda za a ƙarfafa tsaron zirga-zirgar jiragen ruwa sakamakon karuwar hare-haren da ake kai wa jiragen kasuwanci, tankokin mai da sauran muhimman kayayyakin more rayuwa na teku.

A ƙarshe, ƙasashe 14 ne suka sanya hannu kan sanarwar goyon bayan ƙawancen. Waɗannan sun haɗa da Najeriya, Saudiyya, Kuwait, Bahrain, Qatar, Pakistan, Turkiyya, Masar, Jordan, Yemen, Bangladesh, Sudan, Djibouti da Somalia.

Sanarwar ta ce sabon ƙawancen zai mayar da hankali ne wajen kare ‘yancin zirga-zirga a teku, hanyoyin kasuwancin duniya da kuma hanyoyin jigilar makamashi a yankunan Bab al-Mandeb, Red Sea da Gulf of Aden.

Ƙasashen da suka shiga ƙawancen sun jaddada cewa ƙungiyar za ta kasance ta kare kai ne kawai, ba tare da nufin fuskantar wata ƙasa, ƙawancen soja ko wata ƙungiyar ƙasa da ƙasa ba.

A cewar sanarwar, mambobin ƙungiyar za su riƙa musayar bayanan sirri, shirya ayyukan haɗin gwiwa, horaswa, atisayen soja da kuma gudanar da ayyukan tsaron teku tare.

Shigar Najeriya cikin wannan ƙawance na nuna faɗaɗa rawar da ƙasar ke takawa a harkokin tsaron teku, bayan ta dade tana mai da hankali kan yankin Gulf of Guinea da yammacin Afirka.

DA DUMI-DUMI

Bincike Ya Nuna Fiye da Kashi 55% Na Mata a Habasha Suna Goyon Bayan Miji Ya Dinga Dukan Matarsa A Wasu Lokuta

Rahoton ya kuma bayyana cewa 30% na matan da suka taɓa yin aure ko shiga soyayya sun fuskanci cin zarafi ta hanyar duka, fyade ko cin zarafin zuciya. Duk da haka, 58% daga cikinsu ba su nemi taimako ko kai rahoton abin da ya faru ba.

Rarara da Pantami: Idan Makaɗi Ya Ɗauki Kansa Kamar Jagoran Al’umma, Faɗuwarsa Ta Yi Kusa

Waɗanda suka kare Rarara da sunan Musulunci lokacin da Davido ya soke shi, yanzu ya kamata su faɗi gaskiya. Idan za a kare shi saboda Musulunci, to ya kamata kuma a yi Allah-wadai da abin da ya yi wa ɗaya daga cikin manyan malaman Musulunci.

DAN ADAM ABIN TSORO: Takardar karin matsayi (promotion) dinsa abokinsa na kut-da-kut ya shiga email ya goge

DAN ADAM ABIN TSORO: Takardar karin matsayi (promotion) dinsa abokinsa na kut-da-kut ya shiga email ya goge (yi deleting)

NNPC Ta Ɗauki Sabbin Ma’aikata Fiye da 1,000 Har Sun Fara Aiki Bayan Basu Horo Na Shekara Guda – Ojulari

Abin da ya ba su damar ci gaba da zama a NNPC ba takardar aiki ba ce, aikinsu ne da suka nuna cikin shekara guda da suka yi suna aiki ƙarƙashin matsin lamba," in ji Ojulari.

Masana Sun Gano Hanyar Dakatar da Lalacewar Haƙora Ba Tare da Cire Shi ba

Jagorar binciken, Farfesa Margherita Fontana ta Jami'ar Michigan, ta ce maganin yana da matuƙar aminci har ma ga yara masu shekara ɗaya, kuma zai iya taimaka wa yara ƙanana, tsofaffi, masu nakasa da kuma mutanen da ke tsoron zuwa wurin likitan haƙori.

Kanun Labarai

Kotu a Rasha Ta Kwace Kadarori 123 Mallakin Ƙungiyar Kiristoci ta Jehovah’s Witnesses

Sai dai a shekarar 2022, Kotun Kare Haƙƙin Bil Adama ta Turai ta yanke hukuncin cewa haramta ƙungiyar ya saɓa wa doka.

KO KUN SAN? Hadiza Miller, Matar da Ta Wakilci Zariya a Majalisar Dokokin Kaduna a 1983

Hajiya Hadiza Miller ita ce 'yar Majalisar Dokokin Jihar Kaduna da ta wakilci mazabar Zariya a shekarar 1983, a lokacin Jamhuriya ta Biyu.

Biza Da Fasfo: Amurka Ta Gargadi ‘Yan Najeriya Kan Amfani da Hotunan Fasfo da AI Ta Gyara

Sanarwar ta ce kada masu neman biza ko fasfo su yi amfani da AI, filtoci (filters), ko wani nau'in gyaran hoto na dijital yayin ɗaukar hoton fasfo.
spot_img

Labarai masu alaka

Sauran bangarori

spot_imgspot_img